Hajjin 2023: Kaduna Ta Nemi Karin Kujeru Daga Hukumar Jin Dadin Alhazai NAHCON
- Kaduna ta yi alƙawarin neman karin kujerun hajjin bana 2023 guda 500 bayan kujeru 5,987 da aka ware wa jihar
- Shugaban hukumar jin daɗin Alhazai na jihar, Yusuf Yaqubu Alrigasiyu, ya ce suna tsammanin sauran maniyyata zasu cika ragowar kuɗinsu
- Ya kuma yaba wa NAHCON bisa jajircewar da ta nuna wajen tabbatar da kuɗin kujera bai haura miliyam uku ba
Kaduna - Shugaban hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna, Dakta Yusuf Yaqubu Alrigasiyu, ya sanar da cewa hukumar zata nemi karin kujeru 500 a aikin Hajjin bana 2023.
Ya ce zasu nemi wannan ƙarin ne domin cika buƙatun wasu maniyyata da suke tunanin zasu kammala biyan kuɗin kujerar hajji a Kaduna nan da 'yan kwanaki.
Dakta Alrigasiyu Ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai kan shirye-shiryen aikin Hajjin bana ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ya ce tuni hukumar kula da maniyyata ta tarayyan Najeriya (NAHCON) ta ware wa Kaduna kujeru 5,987, tare da yanke kuɗin kowace kujera kan miliyan N2,919,000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka nan ya bayyana cewa duk maniyyacin da Allah ya sa ya gama biyan kuɗin kujera ɗaya kamar yadda aka gindaya, zai samu alawus ɗin tafiya har dala $800.
Meyasa aka samu karin kuɗin kujerar Hajji a 2023?
A jawabinsa, Dakta Alrigasiyu, ya ce akwai muhimman dalilan da suka tilasta aka kara kuɗin kowace kujera, daga ciki harda samar da wurin zama, tashin farashin dala.
Bayan waɗan nan, shugaban hukumar ya ce ƙarin kuɗin harajin VAT da hukumomin Saudiyya suka yi da tsadar litar Man Jirgi na cikin dalilin da yasa aka ƙara ƙuɗin Hajji.
Ya jero sunayen ƙasashe da suka haɗa da, Malaysia, Pakistan, Ghana, da kuma maƙociya Nijar, inda suka ƙara kuɗin Hajjin bana fiye da Najeriya.
Shugaban hukumar walwalar Alhazan Kaduna ya yaba wa NAHCOM bisa namijin kokarinta wajen tabbatar da cewa kuɗin Hajji bai haura miliyan N3m, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
NAHCON Ta Sanar da Kuɗin Kujerar Sauke Farali
a wani labarin kuma Kun ji cewa An Bayyana Kuɗin Kujerar Hajjin Bana 2023 a Najeriya, Ta Kasu Zuwa Gida 8
Hukumar NAHCON a madaɗin gwamnatin tarayya ta sanar da cewa maniyyata zasu biya akalla miliyam N2.8m a matsayin kuɗin kujerar hajjin bana.
Shugaban hukumar ya bayyana kashe-ƙashen farashin kuɗin kujerar a bana, ya danganta da wace jiha maniyyaci ya fito.
Asali: Legit.ng