Ainihin Dalilin Da Ya Sa Orji Kalu Ba Zai Iya Gadon Kujerar Lawan Ba Ta Bayyana
- Yunkurin da Sanata Orji Uzor Kalu ke yi na neman zama shugaban majalisar dattawa ta gamu da barazana daga tsohon sanata daga kudu maso gabas
- Dan majalisar wanda ya wakilci Abia North a majalisa ta 8, Mao Ohuabunwa, ya ce ba za a iya ba Kalu kujerar shugabancin majalisa ba don tuhume-tuhume da EFCC ke masa
- Ohuabunwa, ya cigaba da cewa tsohon gwamnan na jihar Abia ba shi da wani abu da zai amfana mutanensa da shi da wannan mukamin mai karfi
Tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa a Majalisa ta 8, Mista Mao Ohuabunwa, ya ce baya goyon bayan neman shugaban majalisa da Orji Kalu ke yi.
Ohuabunwa, ya ce Kalu, wanda a yanzu ya ke wakiltar Abia ta Arewa, yana da sauran bincike da Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ke yi a kansa kuma an taba samunsa da laifi a baya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abin da ya sa bai kamata Kalu ya zama shugaban majalisa ba, Ohuabunwa ya yi magana
Gabanin kaddamar da Majalisa ta 10 a watan Yuni, Kalu, wanda ya yi nasarar zarcewa, yana daya cikin masu neman kujerar shugabancin majalisa.
Amma, Ohuabunwa, wanda ya yi magana a yayin shirin Politics Today na ranar Litinin, 10 ga watan Afrilu a Channels Television, ya ce tsohon gwamnan na Jihar Abia bai cancani ya wakilci mutane ba.
Abin mamaki, Ohuabunwa ya fito daga mazaba daya tare da Kalu, babban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawan.
Masu neman shugabancin majalisar dattawa suna siyan kuri'un takwarorinsu, Sanata Ndume ya yi fallasa
A wani rahoton, Sanata Muhammed Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin masu neman gaje kujerar Ahmad Lawan sun fara zawarcin takwarorinsu har da siyan kuri'a.
Zababbun sanatocin wadanda ke neman zama shugaba a majalisa zubi ta 10 dai suna ta fitowa suna nuna sha'awarsu na takarar.
Ndume ya yi wannan zargin ne yayin wata hira da kafar BBC Hausa ta yi da shi, yana mai cewa 'a baya dai kuri'un talakawa aka saba siya a yayin zabe amma yanzu abin ta kai ga har kuri'un sanatoci ana siya.'
Asali: Legit.ng