Tashin Hankali: Yan Bindiga A Kano Sun Bi Dare Sun Sace Wani Fitaccen Dan Kasuwa, Sun Bindige Mutum 2
- Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da wani attajiri a kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Kabo a Jihar Kano
- Yan bindigar sun kuma harbi mutum biyu da suka yi yunkurin hana su tafiya da dan kasuwar inda daya ya mutu nan take
- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin sai dai ba ta bada cikakkiyar masaniyar lamarin
Jihar Kano - Wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi dirar mikiya a kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rogo a Jihar Kano, tare da sace wani dan kasuwa Alhaji Nasiru Na'ayya, rahoton The Punch.
Wani shaidar gani da ido kuma dan uwan wanda aka sace da ya nemi a sakaya sunan shi, ya ce yan bindigar sun mamaye yankin tare da harbe-harbe don tsorata mazauna yankin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shaidan gani da ido ya magantu yadda harin ta faru
Ya ce yan bindigar sun yi harbi da ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya bayan da wasu makwabta sun yi kokarin hana guduwa da dan kasuwar yayin da wani ya ji rauni.
"Yan bindigar sun mamaye gidan Alhaji Na'ayya a tsakiyar dare. Sun yi ta harbin iska. Da makwabta su ka yi yunkurin hana tafiya da shi, sun harbi mutum biyu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya nan take yayin da daya ke asibiti yana karbar magani," a cewar shaidar gani da idon.
Wata majiya da ta bukaci a boye sunanta ta ce Gangarbi da makwabtan kauyuka, kamar Bari da Gwangwan na fama da harin yan bindiga a baya bayan nan, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Martanin yan sanda
Da a tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin da tsakar dare amma ya yi alkawarin zai tuntubi majiyarmu da zarar ya samu cikakken bayani akan lamarin.
An Kama Wani Mai Satar Mutane Lokacin Yana Karbar Fansar N3m Daga Hannun Iyayen Wanda Ya Sace
A bangare guda, yan sanda a jihar Filato sun damke wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a lokacin da ya ke kokarin karbar kudin fansa har naira miliyan 3 daga hannun mahaifin wani da ya sace.
Kwamishinan rundunar yan sandan Binuwai Bartholomew Onyeka ne ya fadi hakan a ranar Juma'a lokacin da ya ke zayyana nasarorin da suka samu a rundunar.
Asali: Legit.ng