Yan Bindiga Sun Halaka Ɗan Sanda, Sun Jikkata Wasu Uku a Legas
- Yan bindiga sun yi ajalin jami'an hukumar 'yan sanda, sun jikkata wasu jami'ai uku a yankin Ikorodu a jihar Legas
- A wata sanarwa da jami'an hulɗa na jama'a na rundunar jihar, Benjamin Hundeyin, ya fitar ya tabbatar da lamarin yau Litinin
- Ya ce lamarin ya faru ranar Jumu'a da ta gabata yayin da jami'an yan sandan Caji Ofis ɗin Imiota suka fita sintiri
Lagos - Wasu miyagun 'yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira ranar Jumu'a a yankin Ikorodu da ke jihar Legas, rundunar 'yan sanda ta tabbatar da haka ranar Litinin.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa makasan sun kuma gudu da bindigar ɗan sandan da suka kashe.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) cewa wasu yan sanda uku sun ji munanan raunuka a harin.
Rahoto ya nuna cewa dakarun yan sanda na Caji Ofis din Imiota a yankin Ikorodu na cikin Sintiri lokacin da maharan suka farmake su a mahaɗar Titunan Emuren, kan titin Itokin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasu majiyoyi daga wurin da lamarin ya faru, sun ce makasan, waɗanda ake zargin yaran masu ƙwacen filaye ne sun yi wa yan sandan kwantan ɓauna, suka buɗe musu wuta.
A cewar majiyoyin, nan take maharan suka yi ajalin ɗaya daga cikin 'yan sanda kuma suka yi awon gaba da bindigarsa ta aiki.
"A ranar Asabar, jami'an yan sanda suka kai samame maɓoyar ƙungiyoyin asiri a Emuren, ƙaramar hukumar Shagamu, a jihar Ogun," inji wasu mutane mazauna yankin.
NAN ta rahoto cewa mutane da dama ba basu san hawa ba basu san hauka ba sun gamu da sharrin harin bindiga na wakilan masu kwacen wurare a yankin Ikorodu da kewayenta tsawon lokaci.
Dubu Ta Cika: An Kama Fursunan daYa Gudu da Gidan Yarin Kuje a Nasarawa
A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Kama Fursunan da Ya Gudu daga Gidan Yarin Kuje a Nasarawa
Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta kama wani da ya gudo daga gidan gyaran halin Kuje da abokinsa bisa zargin aikata laifin satar Babura.
Asali: Legit.ng