Kasar Kuwait Ta Haramtawa Limamai Rike Wayoyi Suna Karanta Al-Qur’ani a Lokacin Sallar Dare
- Gwamnatin kasar Kuwait ta bayyana cewa, ta haramta amfani da wayoyin hannu ga limaman da ke jan sallar dare
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da za a fara tsayuwar Tahajjud a masallatan kasar mai adadi da yawa na Musulmai
- Kasar Saudiyya ta bayyana sanya doka kan masu zuwa aikin ibada suna dauke-dauken hotuna a lokacin ziyarar Hajji da Umrah
Kasar Kuwait - An haramtawa limaman masallatai a kasar Kuwait rike wayoyin hannu suna karanta Al-Qur’ani yayin da suke jan nafila a dararen watan, rahoton BBC.
Wannan na zuwa ne daga ma’aikatar wakafi da harkokin addini Islama na kasar yayin da ake tunkarar dararen 10 na karshe a watan mai alfarma.
Rahoto ya bayyana cewa, Salah Al Shilahi, karaminin ministan kula da harkokin masallatai na kasar ne ya fitar sanarwar.
Ministan ya yi wannan bayanin tare da bayyana fa’idojin da wannan dokar za ta kawo ga al’umma da kuma su kansu limaman.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dalilin sanya wannan dokar hana karanta Al-Qur’ani ta waya
A cewar sanarwar ministan, hanin zai amfani limamai sosai, kasancewar hakan zai iya taimaka musu wajen gyaran haddarsu ta littafin mai tsarki, Gulf News ta ruwaito.
Hakazalika, ya ce dokar wata hanya ce ta karfafawa sauran al’umma gwiwa wajen riko da haddar Al-Qur’ani a madadin neman wasu hanyoyi.
A bangare guda, ministan ya nemi dukkan limamai su yi muraji’a haddarsu yadda ya kamata kafin shiga gaban masallaci don jan sallar Tarawih ko Tahajjudi.
Ba wannan ne karon farko da ake sanya dokoki game da ibada ba a duniya, an sha yin hakan a wurare daban-daban, musannan kasashen Musulmai masu riko da addinin da kuma hukumomin da ke kula da harkokin addini.
Saudiyya ta yi gargadi kan masu dauke-dauken hotuna a lokacin ibada
A wani labarin, kunji yadda kasar Saudiyya ta bayyana fushi ga wadanda ke zuwa ibada amma su fake da daukar hotuna a wurare masu daraja.
Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa, ya kamata Musulmai su zama masu mutunta maslalatan harami guda biyu a lokacin da suka kai ziyarar ibada a kasar.
Ba sabon abu bane ganin jama’a suna yawan yada hotunan da suka dauka a lokutan ibadan Hajji ko Umrah ba a kasar ta Saudiyya.
Asali: Legit.ng