Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Arewa Da Ƴan Bindiga Suka Sace Ya Kuɓuta Bayan Biyan Fansa Na Miliyoyi
- Daga karshe Farfesa Onje Gye-Wado, tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane
- Tunda farko rahotanni sun zo kan yadda maharan suka tafi kauyensu su Gye-Wado na Rinza suka yi awon gaba da shi a ranar Alhamis
- Masu garkuwan da farko sun dage sai an biya naira miliyan 70 kafin su sako shi amma daga bisani aka tsaya a Naira miliyan 4, ya kuma koma gida yanzu
Jihar Nasarawa - Farfesa Onje Gye-Wado, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Nasarawa, wanda aka sace a daren ranar Alhamis ya shaki iskar yanci bayan an biya fansar naira miliyan 4.
Legit.ng Hausa ta rahoto yadda aka sace farfesan na Shari'a daga gidansa da ke kauyensu na Rinza, kusa da hedkwatar karamar hukumar Wamba a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wadanda suka sace shi sun nemi a biya Naira miliyan 70, amma iyalansa suka ce Naira miliyan 2 suke da shi, daga bisani aka kara zuwa Naira miliyan 3.5, a karshe aka biya Naira miliyan 4 kafin sako shi.
Wani majiya daga iyalansa ya fada wa Daily Trust cewa:
"Masu garkuwar sun karbi kudin fansar kusa da Mada Hills Secondary School a Akwanga, da katin waya na N200, daga nan suka sako shi daga sansaninsu kusa da Angwan Chiyawa, kusa da duwatsun Akwanga da Nasarawa Eggon."
An tabbatar da sakin Farfesa Gye-Wado
An tattaro cewa an kai Farfesa Gye-Wado fadar babban basaraken Wamba, Oriye Rindire, Mai shari'a Lawal Musa Nagogo bayan sako shi.
Tsohon shugaban kungiyar NUJ kuma tsohon kwamishinan Labarai na jihar, Mista Dogo Shamma, shima ya tabbatar da sakin Farfesa Gye-Wado, ta sakon tes.
Ya ce:
"Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, an sako Farfesa Onje daga hannun masu garkuwa a yanzu."
Masu Garkuwa Da Suka Sace Tsohon Mataimakin Gwamna Sun Nemi A Biya Kudin Fansarsa
A wani rahoton a baya kun ji cewa miyagun yan bindigan da suka bi dare suka sace tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye-Wado sun nemi a biya su Naira miliyan 70 a matsayin kudin fansarsa.
Majiya wacce ke da masaniya kan lamarin ta ce iyalansa sun ce ba su da naira miliyan 70 kuma ba su san inda za su samu ba saboda ana hutun Easter.
Asali: Legit.ng