“Na Hango An Rantsar Da Shi a Matsayin Shugaban Kasa”: Fasto Ya Yi Sabon Hasashe Kan Tinubu

“Na Hango An Rantsar Da Shi a Matsayin Shugaban Kasa”: Fasto Ya Yi Sabon Hasashe Kan Tinubu

  • Shaharran Faston Najeriya, Primate Olabayo, ya yi hasashen cewa za a rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu duk da kalubalen sakamakon zaben
  • Primate Olabayo ya yi ikirarin cewa ya fada ma Tinubu a shekarun baya cewa zai zama shugaban kasa kamar yadda Allah ya nuna masa
  • Malamin addinin ya yarda cewa za a rantsar da Tinubu, koda dai akwai masu adawa da sakamakon

Shugaban cocin Evangelical Church of Yahweh Worldwide, Theophilus Olabayo, ya yi hasashen cewa za a rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na gaba a ranar 29 ga watan Mayu.

Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, da kuri'u fiye da miliyan takwas.

Kara karanta wannan

A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu

Zababben shugaban kasa Bola Tinubu
“Na Hango An Rantsar Da Shi a Matsayin Shugaban Kasa”: Fasto Ya Yi Sabon Hasashe Kan Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sai dai kuma, wadanda suka zo na biyu da uku a zaben, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party suna kalubalantar sakamakon zaben a kotu.

Hakan ya kai ga wani sashi na kira ga kafa gwamnatin wucin gadi, suna korafin cewa bai kamata a rantsar da Tinubu ba har sai kotu ta zartar da hukunci kan karar da Atiku da Obi suka shigar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da wadannan korafe-korafen, Primate Olabayo ya ce za a rantsar da tsohon gwamnan na jihar Lagas.

Yadda na yi hasashen nasarar Tinubu - Primate Olabayo

Primate Olabayo ya ce Allah ya nuna masa kafin zabe cewa Tinubu ne zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

Ya ce ya sanar da zababben shugaban kasar Najeriya, Tinubu a shekarun baya lokacin da suka hadu a Amurka cewa zai zama shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Jawabin Ban Kwana: Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Nigerian Tribune ta rahoto cewa Malamin ya ce kafin zaben shugaban kasa shi ya tambayi Ubangiji wanene zai zama shugaban kasar nan na gaba.

Ya ce:

"Allah ya fada mani cewa daga cikin dukka yan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu ne zai yi nasara.
"A shekarun baya lokacin da na hadu da Tinubu a Amurka, na fada masa cewa lokaci zai zo da zai zama shugaban kasar nan. Bani da wata halaka ta musamman da shi kuma na hadu da shi ne a baya a gidan mamba na. Bana bin ra'ayin mutane, sai dai wanda Allah ya fada mani."

Primate Olabayo ya ci gaba da cewa:

"Na hango an rantsar da shi a matsayin shugaban kasa. Koda dai, kamar yadda na fadi a baya, akwai mutanen da basa so hakan ya kasance."

A wani labari makamancin wannan, Primate Ayodele ya ce za a ranstar da Tinubu a matsayin shugaban kasa kuma ba za a kafa gwamnatin wucin gadi ba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng