Babban Rashi: Buhari Ya Aike Sakon Ta'aziyya Ga Sheikh Sharif Saleh
- Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa kan mutuwar babban dan Sheikh Ibrahim Ibn Saleh al-Hussaini
- Buhari ya bayyana marigayi Alhaji Musa Alkasim a matsayin wani majingina ga Shehin malamin
- Ya yi wa gwamnati da daukacin al'ummar jihar Borno ta'aziyyar wannan babban rashi da suka yi inda ya ce za a dade ba a manta da marigayin ba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Sheikh Ibrahim Ibn Saleh al-Hussaini, kan babban rashi da ya yi.
Shehin malamin wanda shine shugaban kwamitin Fatwa na kwamitin koli na addinin musulunci, ya yi rashi na babban dansa mai suna Alhaji Musa Alkasim.

Asali: Twitter
Buhari ya aike da sakon ta'aziyyar nasa ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar, sashin Hausa na BBC ya rahoto.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba
Ina mika ta'aziyyata ga gwamnati da mutanen jihar Borno, Buhari
Shugaban kasar ya kuma yi ta'aziyya ga gwamnati da daukacin al'ummar jihar Borno kan wannan rashi da suka yi na Alhaji Musa Alkasim.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ila yau, Buhari ya ce ya kadu matuka da samun labarin rasuwar wanda ya bayyana a matsayin wata 'majingina' ga shehin malamin.
Ya kuma bayyana marigayin mai shekara 59 a duniya a matsayin mutum mai halin dattako wanda za a jima ba manta da shi ba.
A karshe ya roki Allah ya yi masa gafara, tare da bai wa iyalansa da al'ummar Borno hakurin jure rashinsa.
Allah ya yi wa mai dakin hamshakin mai kudi Aminu Dantata rasuwa
A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya yi wa matar shahararren dan kasuwa mazaunin Kano, Alhaji Aminu Dantata, Hajiya Rabi Aminu Dantata rasuwa.

Kara karanta wannan
Karfin hali: Yadda makaho ya shige soyayya da tsaleliyar budurwa, ya nemi aurenta
Marigayiyar wacce ita ce matar daya daga cikin shahararrun yaran dattijon kasar wato Tajudeen Dantata ta rasu ne a kasa mai tsarki (Saudiyya). Marigayiyar ita ce matar Alhaji Aminu Dantata ta biyu.
Mama Rabi ta amsa kiran mahaliccinta ne a wani asibitin Jiddah a ranar Asabar, 8 ga watan Afrilu bayan ta yi fama da jinya mai tsawo.
Marigayiya Mama Rabi ta rasu ta bar mijinta, 'yayanta su guda biyar da kuma tarin jikoki masu yawan gaske.
Asali: Legit.ng