Jerin Irin Tufafin Da Aka Haramta Saka Wa A Jami'ar Calabar
- Jami'ar Calabar ta haramta sanya wasu nau'in suturu a makarantar
- Hukumar sadarwar makarantar UNICAL, SERVICOM ce ta sanar da haka biyo bayan karuwar shigar rashin da'a tsakanin dalibai da wasu malamai mata
- Jami'ar ta ce dokar hana sanya nau'in kayan zai fara daga Talata, 2 ga watan Mayu
Calabar, Jihar Cross River - Hukumar jami'ar Calabar (UNICAL) ta kirkiro dokar sanya tufafi a kokarin rage rashin da'a tsakanin malamai da dalibai.
Farfesa Patrick Egaga, daraktan SERVICOM na jami'ar, ya bayyana damuwarsa kan shigar rashin da'ar, musamman tsakanin dalibai da wasu malamai mata, kamar yadda PM News ta ruwaito.
Jerin shiga da aka haramta a Jami'ar Calabar (UNICAL)
1. Gajeren siket ko tufafi
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Riga da bai rufe gwiwa ba, tufafi mai budaden baya da irinsu
3. Spaghetti finger
4. Riguna masu gajeren hannu
5. Handless gowns
6. Bikinis masu nuna sura ko siffan jiki
7. Bum shorts masu nuna cinya
8. Split-skirts
9. Kaya masu matse jiki
10. Riguna masu wuyar V da ke nuna 'tsiraici'
11. Tubes, strip-less
12. Dagargajajen jeans
13. Shorts above the knee
14. Riguna marasa hannu
15. Singlets Lingeries
16. Zazzage wanduna da wasunsu.
Dokar za ta fara daga 2 ga watan Mayu
Jami'ar ta sanar da Talata, 2 ga watan Mayu a matsayin ranar da dokar za ta fara aiki.
Duk dalibin da ya zo da irin shigar ba zai "shiga harabar makaranta ba ko kuma ya karbi hukuncin da ya dace."
"Ba za mu juri irin wannan a cikin jami'ar ba daga Talata 2 ga watan Mayu 2023," in ji Farfesa Egaga.
"Za a kafa jami'an tsaro hadin gwiwa da hukumar gudanarwa don tabbatar da bin dokar" in ji shi.
An bukaci dalibai mata na jami'ar UNICAL da su kwaikwayi shigar shugabar jami'ar
Farfesa Egaga ya ce akwai bukatar dalibai da malamai mata da su kwaikwayi shigar shugabar jami'ar, Farfesa Florence Obi, da mataimakanta, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ya kuma yi kira ga dalibai maza da malamai da su yi koyi da salon shigar shugaban gudanarwar jami'ar, Janar Martin Luther-Agwai mai ritaya, da kuma rajistara, Mista Gabriel Egbe.
Gwamnan Anambra Ya Rufe Gidajen Caca Da Wasanni
A wani rahoton, gwamnatin jihar Anambra ta bada umurnin rufe dukkan gidajen caca da gidajen wasan gyam a jihar.
The Punch ta rahoto cewa gwamnan ya bada umurnin ne bayan samun ayyukan masu aikin damfara.
Asali: Legit.ng