Wani Mutum Dan Shekara 60 Da Yayansa Biyu Sun Lakadawa Jami'an FRSC Duka, Sun Kona Motarsu A Bauchi
- An kama wani mutum mai suna Umar Gwallaga dan shekara 60 da yayansa biyu kan zarginsu da kai wa jami'an FRSC hari da kona motarsu
- Rahotanni sun nuna cewa Umar da yayansu sun taso daga Bauchi zuwa Gombe aka tsare su da safe don bincike amma suka ki tsayawa
- A hanyarsu ta dawowa daga Gombe zuwa Bauchi an sake tsare su an bukaci su nuna takardu, daga nan suka farwa jami'an FRSC da duka har suka kona motarsu
Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda ta kama wani mutum dan shekaru 60 da yayansa biyu, kan kai wa jami'an Hukumar Kiyayye Haddura, FRSC, hari tare da raunata jami'i yayin da suke sintiri.
Jaridar The Punch ta kuma rahoto cewa sun banka wa motar sintirin na FRSC wuta.
Kakakin yan sanda ya magantu kan yadda abin ya faru
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Arewa Da Ƴan Bindiga Suka Sace Ya Kuɓuta Bayan Biyan Fansa Na Miliyoyi
Kakakin yan sanda na Bauchi, Wakil, yayin tabbatarwa yan jarida bayanin cikin hirar wayar tarho ya ce jami'an na FRSC suna aiki na kan hanyar Bauchi zuwa Gombe, suka tsayar da wadanda ake zargin amma suka ki tsayawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce wadanda ake zargin, Umar Gwallaga, dan shekara 60, da yaransa biyu - Nasiru Umar Gwallaga, dan shekara 42, da kaninsa, Usman Umar Gwallaga, dan shekara 39, suna cikin wata mota Mitsubishi Pajero jeep daga Gombe suna Bauchi lokacin da aka tsayar da su.
Wakil, sufritandan yan sanda ya ce:
"A ranar 7 ga watan Maris, 2023, misalin karfe 6 na safe, wani Nasiru Umar, na shekara 42 mazaunin Gwallaga, Bauchi, ya dako iyalansa a motarsa Mitsubishi Pajero jeep daga Bauchi zuwa Gombe.
"Da suka isa kauyen Tashan Durumi, a karamar Hukumar Kirfi, tawagar FRSC da ke sintiri da ke bincika motocci ta tsayar da su amma direban bai tsaya ba.
"Misalin karfe 3 na rana, yayin dawowa daga Gombe zuwa Bauchi, an tsayar da shi an bukaci ya nuna takardun mota, amma ya fito daga motar ya kai wa jami'in FRSC, Anas Aliyu, hari, ya masa targade a hannu.
"Daga nan ya kai wa direban motar sintirin hari kuma ya cinnawa motar wuta, a hakan, mahaifinsa, Umar Ahmed Gwallaga da kaninsa, Usman Gwallaga sun taya shi dukan jami'an."
Ya cigaba da cewa a yanzu suna tsare hannun yan sanda kuma kwamishinan yan sanda, CP Aminu Alhassan ya umurci DPO ya yi bincike, idan an same su da laifi a gurfanar da su kan laifin kona mota a kotu.
Kakakin FRSC ya yi martani
Kakakin yan sandan ya shawari al'umma su rika mutunta jami'ai da ke bakin aikinsu da doka ya umurci su yi.
Kwamandan FRSC, Yusuf Abdullahi, shima ya soki lamarin, yana bayyana shi a matsayin lamari mara dadi.
Abdullahi ya bada tabbacin za a yi bincike a dauki matakin da ya kamata.
Mutan 18 sun kone sakamakon hadarin mota da ya ritsa da su a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutum 18 sun rasu sakamakon mummunan hadarin mota da ya ritsa da su a Bauchi
Lamarin ya faru ne misalin karfe 4.40 na yammacin ranar Laraba a jihar ta Bauchi, rahoton Punch.
Asali: Legit.ng