Hamshakin Dan Kasuwa Alhaji Aminu Dantata Ya Yi Babban Rashi
- Hajiya Rabi Dantata, matar shahararren dan kasuwa Alhaji Aminu Dantata, ta riga mu gidan gaskiya
- Rahotanni sun bayyana cewa Hajiya Rabi wacce aka fi sani da Mama Rabi ta rasu ne a kasa mai tsarki wato Saudiyya bayan jinya
- Sanusi Dantata, jika ga marigayi Hajiya Rabi shima ya tabbatar da rasuwarta cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na sada zumunta na Facebook
Matar dattijon kasa kuma hamshakin dan kasuwa mazaunin Kano, Alhaji Aminu Dantata, Hajiya Rabi Aminu Dantata ta rasu, rahoton Daily Trust.
Marigayiya, wacce aka fi yi wa lakabi da Mama Rabi ita ce mahaifiyar daya cikin shahararrun 'ya'yan Alhaji Aminu Dantata, Tajudeen Dantata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar majiya daga iyalan marigayin, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Jiddah, a kasar Saudiyya, a ranar Asabar.
An kuma ce ta yi fama da rashin lafiya mai tsawo.
Mama Rabi ita ce mata ta biyu ga fitaccen dattijon na kasa.
Yayan da marigayiya Rabi ta haifa wa Alhaji Aminu Dantata
Marigayiyar wacce ta haura shekaru 70 ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya shida da jikoki masu yawa, 'ya'yan sune:
- Tajudeen Dantata
- Batulu Dantata
- Hafsa Dantata
- Jamila Dantata
- Aliya Dantata
Jikan marigayiyar ya tabbatar da rasuwar Hajiya Rabi
Daya cikin jikokin marigayiyan, Sanusi Dantata, shima ya tabbatar da rasuwar ta a sahihin shafinsa na Facebook, ya ce:
"Ku yi wa mamanmu kuma kakanmu Haj. Rabi matar Alh. Aminu Dantata addu'a, ta rasu jiya bayan jinya mai tsawo!
"Allah ya gafarta mata, ya karbi ibadunta, ya saka mata da gidan aljanna mafi daraja. Ameen!.
“Innalillahi Wa Inna Ilaihirrajiuun!”
Dan majalisar jihar Katsina, Honarabul Dakta Aminu Ibrahim Kurami ya rasu
A wani rahoto mai kama da wannan kun ji cewa dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar Bakori, Dakta Ibrahim Aminu Kurami ya riga mu gidan gaskiya.
Kurami ya cika ne a kasa mai tsarki a lokacin da ya tafi yin aikin Umrah kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Wata majiya daga yan uwan marigayin ta tabbatar da rasuwar ta kuma ce ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a birnin Madina kafin ya rasu.
Asali: Legit.ng