Shehu Sani Ya Goyi Bayan Sanata Kalu, Ya Ce a Mika Kujerar Shugaban Majalisa Kudu Maso Gabas
- Burin zama shugaban majalisar dattawa na sanata Orji Kalu ya kara samun armashi gabanin rantsar da shugaban kasa
- Fitaccen tsohon sanata a Arewacin Najeriya, Shehu Sani ya ce, tsohon gwamnan na Abia ya cancanci kujerar shugaban majalisar dattawa
- A cewarsa, inda za a yi duba ga cancanta, to majalisar kamata ya yi ta zabi Sanata Kalu domin maye gurbin Ahmad Lawal
FCT, Abuja – Tsohon sanata a Najeriya, Shehu Sani ya bayyana goyon bayansa ga burin sanata Orji Uzor Kalu na son zama shugaban majalisar dattawa na majalisa ta 10.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Sani ya bukaci jam’iyyar APC da ta aiwatar da tsarin shiyya wajen zaben sabon shugaban majalisar ta dattawa kana a mika kujerar Kudu maso Gabas.
Da yake bayyana hujjarsa da neman daidaito da adalci, Sani ya ce, ya kamata majalisar ta ajiye duk wani batun siyasa ta rungumi gaskiya da adalci.
A mika kujerar shugaban majalisa zuwa Kudu maso Gabas, inji Shehu Sani
A cewarsa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Kujerar shugaban majalisa ya kamata ta tafi Kudu maso Gabas don nuna daidaito da adalci.”
Da yake bayyana zaban Kalu, Sani ya ce yankin Kudu maso Gabas na da ‘yan majalisa masu yawa da ka iya neman kujerar idan aka bi ka’ida da dokar majalisar.
Ya kara da cewa, duk da cewa bai taba kasancewa mamban jam’iyya mai mulki ba, amma zai fi kyau a duba wanda ya dace a ba shi kujerar don kawo ci gaban Najeriya.
Kalu ya fi kowa cancanta ya gaji Ahmad Lawal
A cewar rahoton jaridar Daily Sun, sanata Sani ya bayyana cewa, ya ma fi dadi da armashi a ce gwamnati mai zuwa ta ba Kudu maso Gabas shugabancin majalisar.
Ya ce:
“Babu mutumin da ya dace da tafiyar da harkokin majalisar dokoki da kawo daidaito kamar Orji Uzor Kalu, musamman duba da kokarinsa a matsayin mai ladabtarwa na majalisar dattawa.
“Ni ba dan APC bane amma ina ganin shine mafi cancanta fiye da wadanda suka bayyana burinsu. Kuma Kalu na da gogewa da kwarewa har ila yau.”
An kori sanata a APC saboda cin dunduniyar jam’iyya
A wani labarin kuma, kunji yadda jam’iyyar APC ta kori sanatan jihar Gombe saboda cin dunduniyar jam’iyyar a zaben da aka kammala.
Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, wani kwamitin da APC ta ya titsiye sanatan, amma ya gaza kare kansa daga zargin da ake masa.
Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da kai ruwa rana game da kujerun sanatoci a Arewa bisa zarginsu da cin dunduniyar jam’iyyar a zabukan da suka wuce.
Asali: Legit.ng