Rigima Sabuwa: Tashin Hankali Ya Barke Bayan An Halaka Dalibin Jami'a a 'Hostel'

Rigima Sabuwa: Tashin Hankali Ya Barke Bayan An Halaka Dalibin Jami'a a 'Hostel'

  • An samu hargitsi da tashin hankali sosai a jami'ar Adekunle Ajasin bayan an halaka wani ɗalibi
  • Ana zargin wani ɗan daba da halaka ɗalibin bayan gardama ta ɓarke a tsakanin su kan wasu kuɗi ƙalilan
  • Ɗaliban makarantar sun fusata inda suka fito zanga-zanga domin nuna fushin su kan kisan da aka yi wa ɗalibin

Jihar Ondo - Ɗaliban Jami'ar Adekunle Ajasin, da ke a Akungba-Akoko a jihar Ondo, sun tayar da hargitsi a ranar Alhamis bayan an halaka wani ɗalibi mai suna Temitayo Ayodeji.

Masu zanga-zangar sun cinnawa gidan mahaifiyar wanda ake zargi da kisan wuta, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Jami'a
Tashin Hankali Ya Barke Bayan An Halaka Dalibin Jami'a a Hostel Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mr Ayodeji ya rasa ransa ne bayan wani wanda ake zargin ɗan daba ne mazaunin cikin garin ya caka masa wuƙa bayan gardama ta ɓarke a tsakanin su, a gidajen kwanan ɗalibai da ke a wajen makarantar.

Kara karanta wannan

Zababben Gwamnan APC Ya yi Kus-Kus Da Shugaba Buhari, Ya Ce Jiharsa Na Neman Dauki

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wasu mutane sun bayyana cewa gardamar ta ɓarke ne a tsakanin su kan N1000, duk da dai har yanzu bayanai ba su gama fitowa ba sosai kan lamarin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ɗaliban makarantar na samun labarin mutuwar ɗalibin, sai suka fusata inda nan da nan hankula da tsoro suka cika harabar makarantar.

An samo cewa gidan da mahaifiyar wanda ake zargin ta ke zaune a ciki, fusatattun ɗaliban masu gudanar da zanga-zanga sun cinna masa wuta.

Ɗaliban sun kuma cigaba da gudanar da zanga-zanga a cikin garin na Akungba, a dalilin kisan da aka yiwa ɗan'uwan su.

Sai dai, jami'an ƴan sanda sun yi ƙoƙarin daƙile hatsaniyar tare da haɗin guiwar shugabannin makarantar, inda suka kwantar hankula a cikin jami'ar.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Jami'inta Bisa Halaka Dan Kasuwa Saboda Kudin Cin Hanci

Ta bayyana cewa ɗalibin da aka cakawa wuƙar, an tabbatar da mutuwar sa lokacin da aka kai shi zuwa asibiti.

An Harbe Dalibin Ajin Karshe a Jami'ar UNIBEN Har Lahira a Hostel

A wani labarin na daban kuma, mahara sun halaka wani ɗalibin ajin ƙarshe a jami'a, a ɗakin kwanan ɗalibai.

Ɗalibin ya rasu nan take ne dai a jami'ar UNIBEN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng