'Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Bauna, Sun Kashe Yan Sanda Uku a Jihar Edo
- Miyagun 'yan bindiga sun halaka jami'an yan sanda uku, sun raunata ɗaya a wani sabon hari a jihar Edo
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi wa 'yan sandan kwantan bauna a kusa da babbar kasuwar Agor ranar Alhamis
- Shugaban 'yan bangan yankin ya ce sun bi sawun maharan kuma sun kama ɗaya, sun kwato makamai
Edo - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi ajalin jami'an 'yan sanda uku yayin da wani ɗaya ya samu rauni a wani sabon hari da suka kai musu ranar Alhamis a jihar Edo.
Daily Trust ta tattaro cewa 'yan sandan na kan hanyar zuwa wurin aikinsu sa'ilin da maharan suka musu kwantan ɓauna ba zato ba tsammani a kusa da Agor, kan titin Igarra-Auchi.
Rahoto ya nuna cewa ɗaya daga cikin yan bindigan ya sheƙa barzahu yayin da wani ɗaya ya samu raunukan harbin bindiga, kuma an tafi da shi Asibiti domin masa magani da bincike.
Bayan haka dakarun 'yan sanda sun samu nasarar kwato makamai daga hannun 'yan ta'addan, ciki har da bindigu Shida.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Lamarin ya faru a tsakanin karfe 5:30 zuwa karfe 6:00 na yamma a kusa da sananniyar kasuwar nan ta Agor, wurin da jami'an 'yan sanda suka saba kafa shinge.
Yadda lamarin ya faru
Bayanai sun nuna cewa jami'an 'yan sandan na cikin tafiya a mota, wani abokin aikinsu ɗan sanda na binsu a baya a kan Babur lokacin da maharan suka farmake su.
Amma ɗan sandan dake baya ne ya maida martani har yan bindigan suka gudu da bindigun 'yan sanda huɗu bayan sun yi ajalinsu, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Da yake jawabi kan lamarin, shugaban ƙungiyar 'yan bangan yankin, Ibukun Dogo, yace sun bi sawun makasan ta hanyar amfani da shaidar jinin dake zuba a jikinsu har zuwa maɓoyarsu.
Dogo ya ce sun taras da mutum biyu daga cikinsu ɗauke da raunukan harbin bindiga. Ya ƙara da cewa:
"Ɗaya ya mutu yayin da 'yan sanda suka tafi da ɗayan zuwa Asibiti, mun kwato bindigu 4 da suka tafi da su da kuma ƙarin guda biyu. Wanda ake zargin ya ce daga Okene, jihar Kogi su ka fito."
Yan bindiga sun kai hari jihar Benuwai
A wani labarin kuma Akalla Mutane 46 Suka Mutu a Wani Sabon Mummunan Hari da Aka Kai Jihar Benuwai a Watan Azumi
Wasu yan bindiga da ake zaton muggan makiyaya ne sun kashe rayuka sama da 40 a kauye ɗaya a jihar Benuwai kwana ɗaya bayan sun kashe mutane uku.
Shugaban ƙaramar hukumar yankin da lamarin ya faru ya rasa ɗansa, surukinsa da kuma ɗan kanwarsa a harin.
Asali: Legit.ng