"Dimukradiyya Ce Tsari Mafi Dacewa", Buhari Ya Fada Wa Jakadu A Sakon Bankwana

"Dimukradiyya Ce Tsari Mafi Dacewa", Buhari Ya Fada Wa Jakadu A Sakon Bankwana

  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa duk da juyin mulki da ake yi a sassan Afirika dimukradiyya ce tsari mafi dacewa
  • Shugaban ya bayyana haka lokacin da ya ke karbar bakoncin jakudu biyu da ke bankwana da Najeriya a fadarsa
  • Jakadun na kasashen Angola da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce alaka za ta cigaba tsakanin kasashen da kuma Najeriya

FCT, Abuja - Shugaba Buhari ranar Alhamis ya ce duk da juyin mulki a wasu kasashen Afirika, "dimukradiyya ce tsari mafi dacewa," rahoton Daily Trust.

Shugaban ya bayyana haka yayin ziyarar da jakudu biyu masu barin gado suka kai masa a ziyarar ban kwana, Dakta Eustaquio Januario na Angola da kuma na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) Dakta Obaid Al Taffaq, a gidan gwamnati da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Aika Wasika, Yana Nemawa Sanatan da Aka Samu da Laifi a Ingila Alfarma

Shugaba Muhammadu Buhari
Dimukradiyya Ce Tsari Mafi Dacewa, Buhari. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Buhari, a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya tunatar da irin rawar da Najeriya ta taka ta hanyar amfani da karfinta da ikonta don taimakawa kasar Angola.

Shugaba Buhari, da ya ke karbar bakoncin jakadan UAE, ya ce ya ji dadin yadda Najeriya ke yabonsa, kamar yadda ya bayyana a bayanansa.

Shugaban, da ya ke bada labarin irin tarbar da ya ke samu idan ya ziyarci UAE, ya bada tabbacin kasashen za su cigaba da kyautata alaka, "saboda manufofi iri daya da dama."

Jakadun biyu sun fadi maganganu masu dadi game da zamansu a Najeriya.

Dakta Quibato na jamhuriyyar Angola ya godewa shugaban "saboda irin kyakkyawan mulki da ka ke yi wa Najeriya," saboda zama zakaran yakar rashawa a Afirka, da kuma karya lagon Boka Haram".

Kara karanta wannan

29th May: Shugaba Buhari Ya Ba Da Mamaki, Ya Faɗi Muhimmin Abinda Zai Yi Bayan Miƙa Wa Tinubu Mulki

Jakadun Masu Bankwana Sun Jinjina Wa Buhari

Jakadun ya kuma yabawa Shugaba Buhari bisa yadda ya mayar da Najeriya mai dogaro da kanta.

Dakta Taffaq a na shi bangaren ya yi alkawarin kasashen biyu za su cigaba da aiki tare "game da alakarmu", ya na mai cewa ya samu abokai a ciki da wajen gwamnati, a zamansa na shekara biyar.

Ya ce ya yawata sosai a Najeriya, ya kuma ga bambancin al'adun mutanen kasar.

"Zan tafi ina tuna abubuwa da dama. Zan cigaba da kasancewa makusanci ga Najeriya ta bangarori da yawa," jakadan ya dauki alkawari.

Ba Ka Riga Ka Zama Gwamnan Kano Ba, Ganduje Ya Fada Wa Abba Gida-Gida

A wani rahoton, kun ji cewa Dr Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya gargadi Abba Kabir Yusuf, zababben gwamna mai jiran gado ya dena saka baki kan mulkin jihar a yanzu.

Ganduje ya tunatar da Abba Gida-Gida cewa shine gwamnan Kano har zuwa ranar 29 ga watan Mayu don haka ba shi da ikon bada umurni a abin da ke hurumin gwamnati ne.

Kara karanta wannan

Ahaf: Gwamnatin Buhari ta gano kasashen Turai na daukar nauyin ta'addanci, sun sha suka

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164