Buhari Ya Kori Shugaban NIPC Saratu Umar Kwanaki Bayan Korar Haruna Na NASENI

Buhari Ya Kori Shugaban NIPC Saratu Umar Kwanaki Bayan Korar Haruna Na NASENI

  • Shugaba Buhari ya sallami Saratu Umar dage shugabancin hukumar NIPC tare da nada shugaban rikon kwarya
  • Sanarwar da Femi Adesina ya fitar ta ce, umarnin korar ya fito daga ministan zuba jari da kasuwanci Niyi Adebayo
  • Saratu ta rike hukumar daga watan Yuli 2014 zuwa 2022 inda aka sake nadata a wa'adi na biyu kafin sanarwar sallarmar ta fito

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Hajiya Saratu Umar, Shugaban Hukumar Habbaka Saka Hannun Jari, NIPC, nan take, The Punch ta rahoto.

Hakan yana zuwa ne kwanaki bayan da shugaban kasar ya sallami shugaban hukumar bunkasa kimiyar kere-kere, NASENI, Mohammed Haruna.

Saratu
Buhari Ya Kori Shugaban NIPC Saratu Umar Kwanaki Bayan Korar Haruna Na NASENI. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

An soke nadin Umar ne cikin wata takarda da hadimin Buhari, Femi Adesina ya fitar.

A cewar sanarwar, shugaban kasar ya bukaci jami'i mafi girma a hukumar ya yi jagoranci na rikon kwarya.

Kara karanta wannan

"Dimukradiyya Ce Tsari Mafi Dacewa", Buhari Ya Fada Wa Jakadu A Sakon Bankwana

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ranar 5 ga watan Yuli, 2022, Shugaba Buhari ya amince da nadin Hajiya Saratu Umar a mukamin na wa'adin shekara biyar.

Nadin Saratu na farko

An nada ta a mukamin karon farko cikin watan Yuli, 2014.

A wancan lokacin, fadar shugaban kasa ta sanar da cewa ta na digiri na farko a bangaren Nazarin Tattalin Ariziki daga jami'ar Ahmadu Bello da kuma digiri na biyu a bangaren Kudi da Banki.

Tana da gogewa ta gida da kasashen waje a bangaren da ta kware, da shugabanci, gudanarwa da kuma sha'anin mulki.

A wata sanarwa da Garba Shehu ya fitar a lokacin, ya bayyana Saratu Umar a matsayin goggagiya, wadda zata kawo sauyi, mai tsari, masaniyar tattalin arziki, mai ciyar da zuba hannun jari gaba, kwararriya a harkar fitar da kaya kasashen waje, da ke da ilimi a bangaren banki da sha'anin kudi, hannun jari da bada shawarwari ga yan kasuwa da ma'aikatun gwamnati a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Kutsa Kai Cikin Sakatariyar Jam'iyya Ta Ƙasa a Abuja

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"A kankanin lokacin da ta yi a matsayin shugabar hukumar, ta mayar da hukumar NIPC zuwa hukumar zuba hannun jari ta zamani da kuma rage zurarewar kudade, inda ta yi tattalin Naira biliyan 500, wanda ta samu yabo daga hukumar RMFC."

Buhari Ya Kori Shugaban Hukumar NASENI

Tunda farko, kun ji cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sallami shugaban hukumar Kere-Keren Kimiyya ta Najeriya, NASENI, Mohammed Sani Haruna.

An bukaci ya mika shugabancin zuwa ga jami'i mafi girma a hukumar kamar yadda The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164