Hankula Sun Tashi Yayin Da Mutane Da Dama Suka Yi Batar Dabo Sakamakon Mummunan Hadarin Jirgin Ruwa A Bayelsa

Hankula Sun Tashi Yayin Da Mutane Da Dama Suka Yi Batar Dabo Sakamakon Mummunan Hadarin Jirgin Ruwa A Bayelsa

  • Jirgin ruwa dauke da fasinja da kaya ya nutse a wani kogi da ke Jihar Bayelsa kuma ana cigaba da aikin ceto
  • Lamarin ya faru a Kogin Okoroma da ke Jihar Bayelsa, sai dai har yanzu ba a san adadin da abin ya shafa ba
  • Rundunar yan sanda ta ce ba a shigar da rahoton faruwar lamarin ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoton

Jihar Bayelsa - Wani Jirgin ruwa da ya kwaso mutane daga garin Yenagoa zuwa Okpoama da ke karamar hukumar Brass ta Jihar Bayelsa ya kife ranar Alhamis, 6 ga watan Afrilu yayin da mutane da dama suka yi batan dabo.

Hadarin ya faru a Kogin Okoroma da ke karamar hukumar Nembe na jihar ta Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Jirgin Ruwa
Mutane Da Dama Sun Yi Batar Dabo Sakamakon Mummunan Hadarin Jirgin Ruwa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Asirin Dan Sandan Bogi Da Abokinsa Ya Tonu, Sun Fada Komar Yan Sandan Ainihi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jirgin katakon na dauke da fasinja da kayan su kafin nutsewarsa a tsakiyar kogin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda iyayen yara da ke jirgin ke cigaba da neman yayansu.

Babu a tantance adadin mutanen da suka bace sakamakon hadarin jirgin ba

Ba a san adadin da abin ya shafa ba har zuwa kammala wannan rahoton sai dai ana cigaba da kokarin ceto mutane.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce ba a shigar da rahoton lamarin ga ofishin yan sanda na karamar hukumar Nembe ba.

Rayukan magidanci da matansa biyu da dansa sun salwanta a Neja sakamakon hatsarin jirgin ruwa

A wani rahoton mai kama da wannan, Kimanin mutum bakwai ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a kauyen Zhigiri da ke karamar hukumar Shiroro na jihar Neja.

Kara karanta wannan

To fah: Matukin jirgi ya shiga tasku, maciji ya makale a kujerarsa sadda yake tuki a sama

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, daga cikin wadanda suka riga mu gidan gaskiya kawai wani magidanci wanda ake kira Malam Mu'azu Babangida, matansa na aure biyu sannan da babban dansa.

Mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin Shiroro, Malam Salisu Mohammed Sabo, ya shaida wa yan jarida cewa abin ya faru ne a lokacin da mutanen kauyen suka hanyar zuwa wani gari mai suna Dnaweto da ke makwabtaka da su misalin karfe 4 na yammacin ranar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164