Akalla Mutane 46 Suka Mutu a Wani Sabon Mummunan Hari da Aka Kai Benuwai

Akalla Mutane 46 Suka Mutu a Wani Sabon Mummunan Hari da Aka Kai Benuwai

  • Wasu mahara da ake zargin muggan makiyaya ne sun kashe akalla mutane 46 a kauyen Umogidi, karamar hukumar Otukpo, jihar Benuwai
  • Ɗan shugaban ƙaramar hukumar da wasu masu alaƙa da shi na cikin waɗanda maharan suka kashe a sabon harin
  • Ciyaman ɗin, Bako Eje, ya ce suna cikin jimamin harin farko da aka kashe rai uku, maharan suka sake dawowa

Benue - Rahotanni sun nuna akalla mutane 46 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da aka kai ƙauyen Umogidi da ke yankin Entekpa-Adoka, karamar hukumar Otukpo, jihar Benuwai.

Rahoton Daily Trust ya ce wannan ƙauyen ne dai wasu mahara suka kai farmaki ranar Talata da ta gabata, suka kashe mutane uku.

Harin yan bindiga.
Akalla Mutane 46 Suka Mutu a Wani Sabon Mummunan Hari da Aka Kai Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Bako Eje, wanda ɗansa na cikin waɗanda suka rasa rayuwarsu a sabon harin, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Miji da Mata da Ɗiyarsu Sun Rasu Suna Tsaka da Bacci a Kaduna

Ya ce 'yan bindiga sun yi wa kauyen kawanya karo na biyu awanni 24 kacal bayan harin farko, kana suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Eze ya ce zuwa yanzun (da yammacin ranar Alhamis) sun gamo gawarwakin mutane 46 kuma da yawan mazauna sun ɓata babu wanda ya san inda suka shiga.

Ciyaman ɗin ya kara da cewa ɗansa da wasu 'yan uwansa na cikin waɗanda sabon harin ya rutsa da su wanda ya faru da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin Laraba lokacin da ake kokarin binne mutum 3 na farko.

A rahoton Vanguard, Mista Eje ya ce:

"Bayan harin farko da ya ci rayukan mutane uku, mun je gane wa idonmu halin da ake ciki da kuma binne gawarwakin. Jim kaɗan bayan gama binne su yan ta'addan makiyayan suka dawo kauyen."

Kara karanta wannan

Ta Fashe An Ji: An Fallasa Mutanen da Tinubu Zai Naɗa a Gwamnatinsa Duk da Ba 'Yan APC Bane

"Sun dawo da misalin ƙarfe 4:15 suka kashe wasu mazauna 46 cikinsu har da ɗana mai shekaru 33. Haka nan sun kashe mijin kanwata da ɗanta, wasu da yawa sun ɓata bamu san inda suka shiga ba, har yanzun ina cikin ƙauyen."

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Basarake Mai Martaba a Jihar Filato

A wani labarin kuma A Watan Azumi, 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba a Arewa

Wasu tsagerun 'yan bindigan daji sun kutsa har cikin fada, sun sace mai martaba a masarautar Chip, ƙaramar hukumar Pankshin, cikin jihar Filato.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262