Matashi Ya Ga Tsoho Yana Tura Baro, Ya Gwangwaje Shi Da Kyaututtuka a Bidiyo

Matashi Ya Ga Tsoho Yana Tura Baro, Ya Gwangwaje Shi Da Kyaututtuka a Bidiyo

  • Bidiyon wani matashi da ya taimakawa wani tsoho tare da sauya rayuwarsa ya tsuma zukata a soshiyal midiya
  • An gano dattijon a cikin bidiyon da ya yadu yana kwasan bola tare da tura baro domin samun na dogaro da kai
  • Bawan Allan ya kai shi shagon siyar da kaya sannan ya siya masa kayan masarufi da suka hada da shinkafa da man gyada

Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno lokacin da wani matashi ya taimaki wani tsoho da ya hadu da shi a kan hanya.

Dattijon mai kokarin neman na kai yana kwashe bola tare da zubar da su don samun na daukar dawainiyar iyalinsa.

A bidiyon, mutumin na kwaso bola daga wurare daban-daban sannan yana tura su a kan baro don kaiwa wajen da zai zubar.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Kama Malamin Makaranta Yana Cin Abincin Dalibarsa a Aji, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Matashi ya tallafawa tsoho mai tura baro
Matashi Ya Ga Tsoho Yana Tura Baro, Ya Gwangwaje Shi Da Kyaututtuka a Bidiyo Hoto: @mclaminecoach
Asali: TikTok

Da ya kai wani mataki, sai ya nemi wani dan dakali na bulo ya zauna yayin da wani matashi mai suna @mclaminecoach a TikTok ya isa gare shi don taimaka masa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kai shi shagon siyar da kaya a motarsa inda ya siya masa sabbin tufafi da takalma sannan ya kuma siya masa kayan masarufi kamar su buhuhunan shinkafa da man gyada kafin ya kai shi gidansa.

A cewar mutumin, idan Allah ya yi maka ni'ima, ka zamo alkhairi ga sauran mutane. Ya kuma ba da shawarar cewa yana da matukar muhimmanci ka nuna wa mutum kauna a lokacin da yake raye.

Bidiyon ya haifar da martani daga jama'a wadanda suka jinjinawa wannan karamci nasa sannan suka yi masa addu'a.

"Idan Allah ya albarkace ka, ka zamo alkhairi ga sauran mutane. Mu nuna soyayya gga abokan da ke raye, wannan yana da matukar muhimmanci," ya rubuta.

Kara karanta wannan

"Namijin Duniya": Bidiyon Yaro Dan Watanni 7 Yana ‘Dare Tsani Ya Bar Mutane Baki Bude

Jama'a sun yi martani

@josequeen223 ta ce:

"Na yi koka yayin da nake kallon wannan. Allah madaukakin sarki ya albarkaceka, dan Allah ta yaya za mu iya taimaka masa muma."

@Kadija Kamara 655 ta ce:

"Allah ya ci gaba da buda maka kan taimakonsa da ka yi."

@johndanladilapshak ya yi martani:

"Allah ka taimake shi. Ba zan iya rike hawayena ba."

@Baby Ivy ta ce:

"Allah ya yi maka albarka dan uwana."

Kalli bidiyon a kasa:

Tsohuwa ta samu kyautar miliyan N44 bayan bayyanar bidiyonta cikin kunci

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wasu bayin Allah sun yi karo-karo inda suka tarawa wata tsohuwa da ke cikin kunci zunzurutun kudi har sama da miliyan N44.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng