Sojoji Sun Gano Sabuwar Maboyar Boko Haram, Sun Yi Kaca-Kaca da Ita, Sun Kashe Tsageru 18

Sojoji Sun Gano Sabuwar Maboyar Boko Haram, Sun Yi Kaca-Kaca da Ita, Sun Kashe Tsageru 18

  • Jami’an sojoji sun yi nasarar lallasa ‘yan ta’addan Boko Haram a cikin dajin Sambisa, sun hallaka wani adadi mai yawa
  • Majiya ta bayyana cewa, harin na soji ya faru ne bayan samun bayanan sirri game da sabuwar maboyar ‘yan ta’addan
  • A baya, kunji yadda aka kama wasu ‘yan ta’addan da suka hallaka basarake a jihar Neja bayan sace diyarsa da karbar fansa N1.5m

Bama, jihar Borno - Rundunar sojin Operation Hadin Kai ta yi kaca-kaca da maboyar ‘yan ta’addan Boko Haram da ke cikin dajin Sambisa a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, sun kashe akalla tsageru 18.

Majiya ta gano cewa, jami’an tsaron sun samu bayanan sirri ne game da sabuwar maboyar ‘yan ta’addan, inda aka ce anan suke kitsa hare-harensu a yankin Sheutari da Mutari.

An naqalto cewa, jami’an runduna ta 21 Brigade Bama ta hada kai da ‘yan sa kai na JTF a ranar Talata tare da babbake maboyar tsagerun, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ahaf: Gwamnatin Buhari ta gano kasashen Turai na daukar nauyin ta'addanci, sun sha suka

An kashe 'yan Boko Haram da yawa a Borno
Jihar Borno da ke Arewa maso Gabas | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda sojoji suka farmaki ‘yan ta’addan

A cewar majiya, an lallasa ‘yan ta’addan ne a cikin wani wuri da suke kira Garin Ba’aba, inda aka kashe da yawa daga cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar tsaron ta ce:

“Jami’anmu sun kassara tare da kashe da yawan ‘yan tada kayar baya, jami’an sojoji da ‘yan sa kai na JTF sun ragargaji maboyar da ke cikin dajin Sambisa.”

Wata majiya ta fadi adadin tsagerun da aka kashe

Shi ma da yake bayyana aukuwar lamarin, masanin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana yadda majiya ta shaida masa yadda farmakin ya faru.

A cewarsa:

“A lokacin farmakin, jaruman sojojin sun hallaka ‘yan ta’adda 18.”

Idan baku manta ba, an kashe ‘yan ta’adda da yawa a yankin Sheutari da Mutari a baya-bayan nan yayin da fada ta barke tsakanin tsagerun biyu; ISWAP da Boko Haram.

Kara karanta wannan

PDP, LP, da NNPP Sun Hada Kai Domin Jagulawa APC Lissafi a Zaben Shugaban Majalisa

An kama ‘yan bindiga a jihar Neja

A wani labarin, kunji yadda wasu ‘yan bindiga suka shiga hannun ‘yan sanda bayan da suka hallaka wani basarake tare da sace diyarsa.

Majiya ta ce, an kame mutanen ne bayan samun bayanan sirri, inda yanzu haka suke fuskantar tuhuma mai zafi daga jami’ai.

Jihar Neja na daya daga cikin jihohin da ke fama da yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda, musamman a cikin wadannan shekarun na baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.