Kungiyar Matan Musulmi Sun Koka Kan Yawan Mace-Macen Aure a Arewa

Kungiyar Matan Musulmi Sun Koka Kan Yawan Mace-Macen Aure a Arewa

  • Kungiyar matan musulmi ta magantu a kan yawaitar mace-macen aure tsakanin al'ummar arewa
  • An daura alhakin yawan mutuwar aure da ake samu kan iyaye domin yawanci basa bin koyarwar Allah wajen bayar da auren 'ya'yansu
  • Malama Khadija Ahmed ta shawarci ma'aurata da su daina son kai kuma su zamo masu hakuri da yafiya idan suna so aurensu ya yi karko

Wata kungiyar matan Musulmi mai suna 'Sisters of Jannah' ta nuna matukar damuwa kan yawan mace-macen aure a tsakanin ma'aurata a yankin arewacin Najeriya.

Kungiyar ta nuna damuwarta ne a wajen taronta na Ramadan wanda ta shirya a karo na biyu a jihar Bauchi inda ta tattauna babban batu na mutuwar aure a gidajen Musulmi.

Babbar bakuwa a taron, Malama Khadija Ahmed, ta koka cewa yawancin iyaye su kan yi watsi da koyarwar Al'qur'ani mai girma wajen bayar da auren 'ya'yansu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan PDP, Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa da Wasu Shugabanni 3

Kwai da ke nuni ga rabuwar aure
Kungiyar Matan Musulmi Sun Koka Kan Yawan Mace-Macen Aure a Arewa Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Shawarar malamar ga ma'aurata

Malamar ta shawarci ma'aurata da su ajiye son zuciya, son kai, izza sannan su dunga hakuri, yafiya da magance banbancinsu da hankali, adalci da soyayyar juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A nashi bangaren, Malam Muhammad Suhailu Lawal ya ce hakuri da yafiya, da wadannan dabi'un da ake nunawa makwabta suna nuni ne ga kyawawan dabi'u wajen bautar Allah daya.

Malamin ya kuma shawarci makwabta da su zamo masu kirki, taimako da baiwa makwabtansu kyauta.

Jagorar kungiyar, Hajiya Maryam Garba Bagel, ta shawarci ma'aurata da kada su zamo masu son kai illa su zamo masu adalci da gaskiya don gina gidan aure mai inganci.

Shehin malami ya koka kan yawan mace-macen aure tsakanin matasa

A wani lamari makamancin wannan, Shehin malamin nan na kotun Abuja, Sheikh Ayuba Abubakar ya nuna rashin jin dadinsa kan yawan mace-macen aure da ke kara kamari a tsakanin matasa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Da Dan Basaraken Kano

Malamin ya nuna takaicinsa ne yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara da Afemai Islamic Movement in Abuja ta shirya, yana mai cewa iyaye basa kiyaye dokokin Al-Qur'ani mai girma wajen bayar da auren yaransu.

A wani labarin kuma, jarumar Kannywood, Rakiya Moussa ta bayyana irin soyayyar da take yi wa wani mawaki amma shi bai damu da lamarinta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng