Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Saukar Gaggawa a Abuja

Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Saukar Gaggawa a Abuja

  • Wani jirgin sama da ya ɗauko fasinjoji da dama ya samu tangardar inji jim kadan bayan ya lula sama zuwa Patakwal, babban birnin Ribas
  • Wani fasinja ya bayyana cewa mintuna kaɗan bayan tashin jirgi aka gaya musu su shirya za'a yi saukar gaggawa a birnin tarayya Abuja
  • Ya ce da farko an ƙi faɗa musu abinda ya faru amma da matuƙan suka ga uwar bari sun gaya musu komai

Abuja - Wani Jirgin sama mallakin kamfanin Aero Contractors, a ranar Laraba da safe, ya gamu matsala a sararin samaniya wanda ya tilasta masa juyo wa cikin gaggawa ya sauka a Abuja.

Wani Fasinjan jirgin da lamarin ya shafa ya shaida wa Leadership ta bayan fage cewa Jirgin saman ya yunkura ya tashi zuwa sararin samaniya da misalin ƙarfe 8:40 na safe.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

Jirgin saman Aero.
Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Saukar Gaggawa a Abuja Hoto: leadership
Asali: UGC

Ya ce mintuna kaɗan bayan tashinsu zuwa Patakwal, matuƙin jirgin ya sanar da cewa an samu tangarɗa zai juya akalar jirgin ya koma babban birnin tarayya Abuja.

Fasinjan ya bayyana cewa duk mutanen dake cikin jirgin ba bu wanda ya san matsalar da jirgin ya samu har sai da Matuƙin ya ga da wuya ya isa sauka lami lafiya a Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wace matsala jirgin saman ya samu bayan ya lula sama?

A kalaman Fasinjan, ya ci gaba da cewa:

"Daga baya muka gano cewa Injin jirgin ne ya samu matsala kamar na'urar da ake amfani da ruwa ce ta ke zuba ko wani abu makamancin haka."
"Lamarin akwai tashin hankali babba, mutane da yawa da ke cikin jirgin sun fara kuka suna bayyana fatansu da addu'a taƙarshe. Amma duk da haka mun yi nasarar sauka a Abuja duk da wahalar da aka sha."

Kara karanta wannan

To fah: Matukin jirgi ya shiga tasku, maciji ya makale a kujerarsa sadda yake tuki a sama

Gwamnoni da Mambobi Na Goyon Bayan Wase Ya Zama Kakakin Majalisa, Buni

A wani labarin kuma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana goyonsa ga takarar Ahmed Idris Wasa a majalisar dokokin tarayya.

Gwamnan ya ce lokaci ya yi da uwar jam'iyya zata sakankawa Idris Wake bisa halacci da biyayyar da ya nuna mata a baya.

Ya ce kamar yadda Wasu ya janye a baya, duk wanda yake neman takarar ya kamata ya janye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262