Tsagerun Yan Bindiga Sun Sace Mata Da Dan Hakimin Kauyen Kano
- Wasu yan bindiga da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne sun farmaki gidan hakimin kauyen Nasarawa a karamar hukumar Tsanyawa, jihar Kano
- Maharan sun sace Halima Kabiru wacce mata ce ga basaraken da kuma dansa mai suna Dahiru Kabiru
- Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar al'amarin inda ta ce tuni ta tura wata tawaga domin ceto mutanen ba tare da kwarzane ba
Kano - Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutum biyu cikin iyalan hakimin kauyen Nasarawa da ke yankin karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Wadanda yan bindigar suka sace sun hada da matarsa mai suna Halima Kabiru mai shekaru 38 da kuma dansa mai suna Dahiru Kabiru dan shekaru 20 a duniya.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta yi martani
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mista Mamman Dauda wanda ya tabbatar da lamarin ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A ranar 2 ga watan Afrilu, da misalin karfe 12:45 na dare mun samu labarin cewa wasu yan bindiga bakwai sun farmaki gidan hakimin kauyen Nasarawa sannan suka yi garkuwa da mata da dansa.
"Masu garkuwa da mutanen sun dauki wadanda abun ya ritsa da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.
"Nan take muka shirya wata tawagar agaji. Yanzu haka da muke magana, tawagar na aiki ba ji ba gani don ceto mutanen da abun ya ritsa da su cikin koshin lafiya."
CP Dauda ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici amma ya nuna karfin gwiwar cewa za a ceto mutanen sannan a kama wadanda suka sace su, rahoton The Guardian.
Yan bindiga sun farmaki al'umomin jihar Neja, sun yi mummunan ta'adi
A wani labarin kuma, mun ji cewa tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai wani kazamin hari kan wasu garuruwan jihar Neja.
Yan bindigar sun kashe mutane bakwai a harin da suka kai kan garuruwa bakwaiu a karamar hukumar Mashegun da ke jihar ta arewa maso tsakiya, sun kuma yi awon gaba da mutane masu yawan gaske.
An tattaro cewa mazauna yankunan da abun ya faru duk sun gudu sun bar gidajensu inda suka koma sansanin yan gudun hijira da ke yankin Kontagora da kewaye domin samun mafaka.
Asali: Legit.ng