Makwabta Sun Maka Zakara a Kotu Saboda Yawan Cara a Kano, An Umurci Mai Zakaran Ya Yanka Shi Ranar Juma'a
- Kotun Kano ta umurci wani mutumi mai suna Isyaku Shu'aibu da ya yanka zakaransa a ranar Juma'a
- Makwabtan Shu'aibu sun yi kararsa a kotu bisa zargin cewa zakaransa yana hana su walawa domin ya cika kiriniya da cara
- Mai shari'a Halima Wali ta kotun majistare da ke unguwar Gidan Murtala ce ta yanke hukuncin a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu
Kano - Wata kotun majistare a jihar Kano ta umurci mamallakin wani zakara da ya yi kaurin suna saboda yawan caransa da ya yanka shi.
Kotun ta ba da umurnin ne a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu bayan wasu makwabtan mai zakaran biyu sun shigar da kara kotu, jaridar Premium Times ta rahoto.
Sun yi ikirarin cewa yawan caran da zakaran ke yi yana hana masu bacci da zaman lafiya a unguwar.
Kotun wacce ke zama a Gidan Murtala ta umurci Isyaku Shu'aibu, mai zakaran da ya yanka shi a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin shigar da karan mai zakaran kotu
Daya daga cikin masu karan, Yusuf Muhammed, na unguwar Ja’en da ke garin Kano ya fadama kotu cewa caran da zakaran ke yi ba kakkautawa yana tauye masa yancinsa na yin bacci cikin jin dadi, rahoton Nigerian Tribune.
Yayin da yake amsa laifin cewa zakaransa na caara da yawa, Mista Shu'aibu ya roki kotu da ta tsayar da hukuncin har zuwa ranar Juma'a.
Mai shari'a Halima Wali, da ta gamsu da muhawarar masu karar, ta yanke cewa a sanya zakaran a akulki sannan a yanka shi a ranar Juma'a.
Uwa ta koka bayan diyarta ta hada mata wuri, ta yi wa kanta matsuguni a durowa
A wani labarin, wata uwa ta koka a shafin soshiyal midiya bayan ta shiga falonsu tare da tarar da karamar diyarta tana yi mata barna da aika-aika.
Yarinyar dai ta fito da duk wayoyin da ke cikin durowan jikin talbijin na dakin sannan ta nemawa kanta wajen a zama a cikinsa tana mai aika-aikanta hankali kwance.
Iyaye da dama da suka yi martani ga bidiyon sun bayyana cewa haka suma suke fama da nasu yaran a gidajensu.
Asali: Legit.ng