Ndume Ya Fallasa Siyan Kuri'u Da Masu Neman Takarar Shugaban Majalisa Ke Yi Don Su Cimma Burinsu

Ndume Ya Fallasa Siyan Kuri'u Da Masu Neman Takarar Shugaban Majalisa Ke Yi Don Su Cimma Burinsu

  • Sanata Muhammad Ali Ndume, daga jihar Borno ya yi ikirarin cewa masu neman kujerar shugabancin majalisar suna siyan kuri'un takwarorinsu
  • Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa da kafar BBC Hausa ta yi da shi
  • Ndume ya ce yanzu ba talakawa ne kadai ake siyan kuri'unsu ba har ma da sanatoci, yana mai cewa da kwarewarsa da yana da kudin siyan kuri'ar da ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Muhammad Ali Ndume, ya yi zargin wasu masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawan sun fara siyan kuri'un takwarorinsu, Daily Trust ta rahoto.

Zababbun sanatoci sun fara zawarcin kujerar shugaban majalisar gabanin kaddamar da majalisar tarayya zubi ta 10 a watan Yunin 2023 ta hanyoyi daban-daban.

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Kulla-Kular Da 'Yan Siyasa Ke Yi Domin Samun Shugabancin Majalisa

Ndume
Ndume ya ce wasu sanatoci na siyan kuri'un takwarorinsu don neman kujerar shugabancin majalisa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma, a wata hira da aka yi da shi a BBC Hausa, Ndume ya yi ikirarin cewa wasu sanatocin na amfani da kudi domin neman goyon baya a maimakon cancanta.

Ya ce:

"A baya, ana cewa kuri'ar talaka ne ake siya, yanzu ta kai matsayin da har kuri'ar sanata ma ana son siya.
"Akwai sanatoci da ke neman darewa kujerar shugaban majalisar dattawa da ke raba wa sanatoci kudi."

Da ina

Ya kara da cewa:

"Idan da ace inda da kudi kuma zan iya rabon kudin yadda ake yi yanzu a majalisa, da kwarewa ta, ina fada maka zan iya zama shugaban majalisar dattawa. Babu wani batun duba cancanta, komai ya koma batun kudi."

Sanata Ndume ya ce Ameachi ya fi kowa dacewa ya yi takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Manyan Arewa Sun Fusata, Sun Aike da Muhimmin Sako Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

A wani rahoton daban, Sanata Muhammad Ali Ndume, shugaban kwamitin harkokin sojoji ta majalisar dattawa ya magantu dangae da takarar da Amaechi ya ke yi a APC.

Da ake zanta wa da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV, Muhammadu Ali Ndume ya ce ya taka muhimmin rawa wurin ganin Amaechi ya shiga takara.

Ya kara da cewa ya yi imanin Mista Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas zai dace da shugabancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164