An Ga Bakin Motocin Sojoji a Najeriya, Hedkwatar Tsaro Ta Yi Bayani Kan Halin Da Ake Ciki

An Ga Bakin Motocin Sojoji a Najeriya, Hedkwatar Tsaro Ta Yi Bayani Kan Halin Da Ake Ciki

  • Motocin Majalisar Dinkin Duniya da aka gani a Benin, jihar Edo na aikin wanzar da zaman lafiyar UN ne, cewar Hedkwatar tsaro
  • Rundunar sojin Najeriya ta baiwa jama'a tabbacin cewa babu wani abun tashin hankali dangane da kasancewar motocin a Benin
  • DHQ ta ce kasar bata karkashin kowace barazana da za ta sa a turo dakarun sojojin UN

An baiwa yan Najeriya tabbacin cewa babu bukatar su daga hankalinsu kan kasancewar motocin sojin Majalisar Dinkin Duniya da wasu mazauna Benin, jihar Edo suka gano.

A wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau, mukaddashin daraktan labaran rundunar tsaro ya saki a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu, rundunar sojin ta bayyana cewa babu wani abun tashin hankali, rahoton Punch.

Dakarun sojoji
An Ga Bakin Motocin Sojoji a Najeriya, Hedkwatar Tsaro Ta Yi Bayani Kan Halin Da Ake Ciki Hoto: Oasis Magazine
Asali: UGC

DHQ ta yi martani

Da yake martani ga bidiyo na wasu motocin yakin UN da aka gani a Benin, Gusau ya ce motocin sojojin sun kasance a kasar ne saboda Najeriya na bayar da gudunmawar dakaru ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daban-daban.

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi: Tsohon Minista a Najeriya Ya Yi Babban Rashi, Mahaifiyarsa Ta Mutu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewar na ba-bayan nan ita ce rundunar wucin gadi na Majalisar Dinkin Duniya a Abyei (UNISFA), Kudancin Sudan.

Birgediya Janar din ya kuma bayyana cewa dan Najeriya, Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr ne ke jagorantar wannan aiki, rahoton Blueprint.

"Ya kamata a lura cewa UN bata da nata dakarun sojin, maimakon haka tana shiga yarjejeniya da dakarun kasashen da ke bayar da gudunmawa don su gabatar da jami'ai da kayan aikinsu a ayyukanta mabanbanta.
"Saboda haka, ya zama dole mu sanar da cewar motocin yakin soji da kayan da aka yi wa fenti da kalar Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda aka gani an shigo da su ne ta tashar jirgin ruwan Warri zuwa yankin da ake aiki a Kudancin Sudan don hadewa da dakarunmu wadanda aka shigar cikin tawagar UNISFA a watan jiya."

Kara karanta wannan

Rai Baƙon Duniya: Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Rasu a Abuja

DHQ ta magantu kan bidiyon Ado-Doguwa yana harbi da bindigar AK-47

A wani labarin kuma, mun ji cewa hedkwatar tsaro ta ce an dauki bidiyon da ke nuna Ado-Doguwa yana harbi ne a sansanin sojoji da ke dajin Falgore.

Ta ce an dauki bidiyon ne a lokacin wani atisaye na rundunar wanda aka gayyaci shugaban masu rinjaye a majalisar a matsayin babban bako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng