Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matar Basarake da Dansa a Jihar Kano
- 'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun yi awon gaba da iyalan Dagacin Nasarawa, karamar hukumar Tsanyawa a Kano
- Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Mamman Dauda, ya tabbatar da lamarin, ya ce maharan sun sace matar Basaraken da ɗansa
- Ya bayyana cewa bayan sun samu labari da tsakar dare ranar 2 ga watan Afrilu, suka tura tawaga ta musamman don ceto waɗanda aka sace
Kano - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum biyu daga cikin iyalan gidan Dagacin ƙauyen Nasarawa, ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.
Ptemium Times ta rahoto cewa waɗanda maharan suka sace sun ƙunshi matar Basaraken, Halima Kabiru, mai shekaru 38 da kuma ɗansa, Ɗahiru Kabiru, ɗan shekara 20.
Kwamishinan rundunar yan sandan jihar, CP Mamman Dauda, ya tabbatar da garkuwa da mutanen biyu ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).
A kalamansa, kwamishinan ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"A ranar 2 ga watan Afrilu, 2023, da misalin ƙarfe 12:45 na tsakar dare muka samu labarin cewa wasu tsagerun 'yan bindiga su Bakwai sun shiga gidan Dagacin Nasarawa kuma sun yi awon gaba da matarsa da ɗansa."
"Maharan da ake zaton masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa ne sun tafi da mutanen biyu zuwa wani wuri da ba'a sani ba har yanzu."
"Bayan samun wannan bayanin nan take muka shirya tawagar dakarun ceto daga Ofisoshi masu maƙotaka da garin. A yanzu da nike magana da ku tawagar dakarun na kan aikin ceto waɗan da aka sace cikin ƙoshin lafiya."
Shugaban rundunar 'yan sandan jihar Kano ya bayyana harin yan bindigan da sace iyalan Basaraken da babban abun takaici wanda ba'a so ba.
Amma CP Mamman Dauda ya jaddada kwarin guiwarsa cewa za'a kubutar da waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya kuma masu garkuwan zasu shiga hannu.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dalibai Kusan 10 a Jihar Kaduna
A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da cewa mahara sun yi awon gaba da ɗalibai kusan 10 a yankin Kachia
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce rahoton farko da suka samu daga hukumomin tsaro ya tabbatar da sace ɗaliban.
Asali: Legit.ng