Mutuwa Rigar Kowa: Mahaifiyar Tsohon Minista a Najeriya Ta Mutu

Mutuwa Rigar Kowa: Mahaifiyar Tsohon Minista a Najeriya Ta Mutu

  • Mahaifiyar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, ta mutu tana da shekaru 75 a duniya ranar Litinin
  • A wata sanarwa mai ɗauke da sannun tsohon ministan, ya ce mahaifiyarsu ta mutu cikin salama zagaye da iyalanta a gidanta da ke Legas
  • Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba iyalai zasu sanar da shirye-shiryen binne marigayya Mama Osi

Lagos - Deaconess Victoria Nneka Chidoka, Mahaifiyar tsohon ministan sufurin jiragen sama a Najeriya, Osita Chidoka, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 75 a duniya.

Shugabar iyalan gidan Chidoka ta mutu ne ranar Litinin 3 ga watan Afrilu, 2023 a gidanta da ke Ikeja, babban birnin jihar Legas bayan fama da rashin lafiya, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Mahaifiyar tsohon minista.
Mutuwa Rigar Kowa: Mahaifiyar Tsohon Minista a Najeriya Ta Mutu Hoto: PM News
Asali: UGC

Tsohon ministan ne ya tabbatar da mutuwar mahaifiyarsa a wata sanarwa mai taken, 'Sanarwan rasuwar Deaconess Victoria Nneka Chidoka,' ɗauke da sa hannunsa.

Kara karanta wannan

Rai Baƙon Duniya: Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Rasu a Abuja

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A rahoton PM News, Sanarwan ta ce:

"Cikin ƙunci da raɗaɗin zuciya da cikakken imanin miƙa lamari ga Allah, muna sanar da rasuwar mahaifiyarmu, 'yar uwa kuma kakarmu, Deaconess Victoria Nneka Chidoka."
"Ta rasu tana da shekaru 75 a duniya ranar Litinin 3 ga watan Afrilu, 2023. Mama Osi kamar yadda aka saba kiranta ta cika cikin kwanciyar hankali kuma zagaye da iyalanta."
"Rai ya yi halinsa yayin da iyalai, yan uwa da abokan arziƙi da masoya suka kewaye ta, wanda ya kawo karshen kalubalen rashin lafiya da ta sha fama da su a karshen rayuwarta."

Chidoka a madadin iyalan gidansu ya ƙara da cewa, "A wannan lokacin muna roƙa mata soyayyar Allah, rahama da salama da sauran iyalan da ta bari a baya."

"Nan ba da jimawa ba iyalanta zasu sanar da shirye-shirye binne ta a lokacin da ya dace."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar Jam'iyya, Sun Kwace Iko Da Ita

Daga cikin 'ya'yan da ta mutu ta bari har da ɗan majalisar wakilan tarayya, Honorabul Obinna Chidoka, mai wakiltar mazaɓar Idemili ta arewa/Kudu a jihar Anambra.

Uwar gidan Sanata Orji Kalu ya rasu

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan jihar Abiya, Sanata Orji Uzo Kalu, ya yi babban rashi a cikin iyalansa

Uwar gidan Sanatan, Misis Ifeoma Kalu.ta kwanta dama tana da shekaru 61 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262