FG Ta Amince Da Manhajojin Bada Bashi 173, Ta Rufe Haramtattun Bankunan Intanet
- Gwamnatin tarayya ta sahalewa manhanjoji 173 bayar da lamuni bayan sun cika ka'idojin da hukumar FCCPC ta sanya
- An ba wa 54 sahalewa bisa wasu sharudda yayin da 119 ke da cikakkiyar sahalewar bayar da lamunin
- Hukumar FCCPC ta sanya wa'adin 27 ga watan Maris a matsayin ranar da za a kammala rijista, bayan cikar wa'adin ta fitar da jerin halastattun manhanjojin da aka sahelawa bayar da lamunin
FCT, Abuja - Hukumar Gasa Ta Tarayya da Hukumar Kare Masu Siyayya ta amince da manhanjojin bada lamuni na zamani 173 su yi aiki a kasar, rahoton The Punch.
Daga 173, 119 na da cikkakiyar sahalewa yayin da 54 ke da sahalewa bisa sharadi. Bayan da manhanjojin bada lamuni suka fara damun yan Najeriya, hukumar FCCPC ta fara musu rijista don kare yan kasa daga fadawa manhajar zamba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta fitar da 'takaitacciyar doka/yin rijista da ka'idojin bada lamuni na zamani 2022' don daidaitawa tare da sanya sharadin yin rijista ga duk kamfanin da ke sha'awar cigaba da tsarin.
Bayan kara wa'adin rajistar karo da dama, da karshe an tsayar da 27 ga watan Maris, a matsayin ranar rufe rajistar.
Hukumar ta saki jerin manhanjojin da aka amince su yi aiki a kasar. Kamfanonin da ba su da rijista ba za su samu damar yin aiki ba.
Da ta ke bayani kan kokarinta akan manhanjojin bada lamuni a Augustan 2022, FCCPC ta ce:
"Kari kan dokokin da muka kafa da kuma kokarin tabbatar da adalci, budadde kuma abin da zai amfani masu bada bashi zuwa masu karba, an samar da hadin gwiwar hukumomi don tantance tare da kafa takaitacciyar doka/rijista da kuma ka'idojin bayar da bashi na zamani, 2022 a matsayin matakin farko na samar da sahihiyar hanya.
'Matsalolin' Najeriya Na Hana Ni Barci, Har Na Kamu Da Rashin Lafiya, Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman
"Wannan ya zama dole. Akwai bukatar izini kafin a cigaba da bayar da lamuni; an samar da wa'adi don masu wannan kasuwanci su yi rijista ko su dakatar da bada lamunin.
"Ka'idojin sun kuma tilasta sauran wanda ke da alaka tsarin (kamar bankuna, shafukan dauko manhajar/ko cike bayanai, masu hakkin mallakar yanar gizo da kuma tsarin biyan kudi) da su tabbatar sun samu sahalewa kafin gudanar da aikinsu."
Wasu cikin bankuna da aka amince wa bada bashi
Daga cikin wanda aka sahalewa bayar da lamunin akwai, Branch International Financial Services Limited, Fairmoney Micro Finance Bank, Pivo Technology Limited, Renmoney Microfinance Bank Limited, Carbon Microfinance Bank Limited, Creditwave Finance Limited da wasu.
Za a soke duk wata manhajar bayar da bashi da ba ta da rijistar FCCPC daga Play Store mallakar kamfanin Google kuma ba a iya dauko shi ba.
A watan Nuwamba, kamfanin Google ya bada sanarwa ga masu dora manhaja, wanda ya tilasta duk masu manhajar bayar da lamuni a Najeriya, India, Indonesia, Philippines da Kenya cewa dole ne su kiyaye ka'idojin da aka sanya.
An yi tsammaci fara aikin dokar ranar 31 ga watan Janairu, 2023. A watan Maris, Google ya soke daruruwan manjahar bayar da lamuni daga Play Store a kasar Kenya kamar yadda TechCrunch ta ruwaito.
A Fabarairun 2023, hukumar Nigeria Data Protection Bureau ta sanar da kafa wani kwamiti, da ya tara hukumomin gwamnatin tarayya, ya na aiki don kawar da ayyukan haramtattun manhanjojin bayar da lamuni a kasar.
Asali: Legit.ng