Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Yi Mutuwar Farat Ɗaya a Abuja

Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Yi Mutuwar Farat Ɗaya a Abuja

  • Tsohon mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Wapkerem Maigida, ya rasu
  • Rahotanni sun bayyana cewa Marigayin ya cika ne bayan yanke jiki a birnin tarayya Abuja, iyalan gidansa sun ce lafiyarsa kalau
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar sojin saman Najeriya ya tabbatar, ya ce labarin mutuwar ya kaɗa rundunar baki ɗaya

Abuja - Tsohon mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya da ya gabata, Air Commodore Wapkerem Maigida, ya riga mu gidan gaskiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Maigida ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi a babban birnin tarayya Abuja.

Maigida.
Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya, Air Commodore Wapkerem Maigida Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wata majiya daga cikin iyalan gidan marigayin, wanda ya tabbatar da ci gaban, ya bayyana cewa babban jami'in rundunar sojin na cikin ƙoshin lafiya gabanin faruwar lamarin.

Kakakin rundunar sojin na yanzu (wanda ya gaji mamacin), Air Commodore Ayodele Famuyiwa, ya tabbatar da rasuwar Sojan, inda ya ayyana rashin da babban abun kaɗuwa.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar Jam'iyya, Sun Kwace Iko Da Ita

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya karbi muƙamin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar Sojin sama da a cikin watan Janairu.

Marigayi Maigida, wanda ya kasance kwamandan rundunar NAF ta 551 da ke sansani a Jos, babban birnin jihar Filato, ya karbi ofishin kakaki daga Air Commodore Edward Gabkwet.

Haka zalika ya yi aiki a matsayin Muƙaddashin Darekta, sashin yaɗa labarai na hedkwatar tsaro kafin daga bisani a sauya masa wurin aiki zuwa Jos a 2022.

Mamacin ya yi digiri na biyu a fannin ilimin kimiyyar tsaro da dabaru da digirin farko a fannin tarihi duk a makarantar sojojin Najeriya NDA.

Haka nan ya yi karatun Diploma a bangaren Public Relations and Advertisement a makarantar horar da 'yan jarida da ke jihar Legas, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Uwar gidan tsohon gwamnan Abiya ta rasu

Kara karanta wannan

Sirri Ya Fasu: An Gano Sunan Gwamnan Arewa da Wasu Mutum 2 da Tinubu Zai Ba Manyan Muƙamai Na Farko

A wani labarin kuma Tsohon Gwamna Kuma Fitaccen Sanatan APC Ya Yi Babban Rashi a Iyalansa

Allah ya yi uqar gidan tsohon gwamnan jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya, Sanata Orji Uzo Kalu, rasuwa tana da shekara 61 a duniya.

Kamar yadda Sanatan ya wallafa a shafinsa na Facebook, yace marigayyar mutumiyar kirki ce mai bautar Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262