Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Har 3 a Jihar Adamawa

Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Har 3 a Jihar Adamawa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku a wani yankin karamar hukumar Hong
  • Wannan lamari na zuwa ne a wani kazamin harin da ‘yan bindiga suka kai da daren jiya Lahadi 2 ga watan Afrilu
  • A bangare guda, wasu ‘yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun sace wasu daliban jami’a, sun tafi dasu cikin daji

Jihar Adamawa - An tabbatar da kisan mutane uku a wani kazamin harin da ‘yan bindiga suka kai Dabna da ke yankin Dugwaba a karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

Rundunar ‘yan sandan jihar ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar da ta ba manema labarai a ranar Litinin a Yola, rahoton Leadership.

A cewar rundunar, yanzu haka an tura jami’ai da kayan aikin da suka dace domin tabbatar da kamo wadanda suka aikata laifin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun harbe shugaban APC a wata jiha, sun hallaka mazauna kauye

Yadda aka kai mummunan hari Adamawa
Jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kwamishinan ‘yan sanda ya yi Allah-wadai da harin

Hakazalika, sanarwar ta ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Afolabi Babatola ya yi Allah-wadai da harin, The Street Journal ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta ce:

“Wasu ‘yan bindigan da ba a san ko su waye ba sun kai kari a daren Lahadi, inda suka farmaki al’umma na bacci suka yi harbin kan mai uwa da wabi kan jama’a.
“Biyo bayan harin, kwamishinan ‘yan sanda ya umarci a gaggauta kamo wadanda suka aikata laifin tare da binciken lamarin don tabbatar da zaman lafiya da adalci.”

Daga karshe, kwamishinan ya yi kira ga a zauna lafiya, a yi hakuri tare da ba jami’an tsaro hadin kai wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

Yadda aka sace ‘yan mata daliban jami’a a jihar Zamfara

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An sace 'yan mata 2 a gidan kwanan daliban jami'ar tarayya a jihar Arewa

A wani labarin, kunji yadda wasu tsagerun ‘yan ta’adda suka kai farmaki dakin kwanan dalibai na jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Harin ya zo da mummunan lamari, inda aka sace wasu dalibai mata biyu; Zainab da Maryam, an tafi dasu cikin dajin da har yanzu ba a san inda suke ba.

Ya zuwa yanzu, ‘yan sanda na ci gaba da bincike don gano inda aka tafi da daliban tare da kokarin tabbatar an ceto su ba tare da wata illa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.