Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sanya Dokar Ta Baci a Wata Karamar Hukuma a Jihar
- Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya doke hana shiga da fita a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar
- Gwamnatin ta sanya dokar kullen ne a Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniyya cikin ƙaramar hukumar ta Chikun
- Gwamnatin tace ta sanya dokar ne bayan an samu asarar rayuka biyo bayan tashin wata rigima
Jihar Kaduna- Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar ta ɓaci ta sa'a 24 a Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniyya cikin ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.
A cewar gwamnatin jihar, ta yanke wannan hukuncin ne bayan an samu ɓarkewar tashin hankali wanda yayi sanadiyyar halaka mutum biyu. Rahoton Daily Trust
Kwamishinan cikin gida da tsaron jihar, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ya bayyana cewa an ba jami'an tsaro umurni da su tabbatar da sun sanya an bi wannan dokar a yankin.
Ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike domin dawo da doka da oda a inda lamarin ya shafa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya buƙaci al'ummar yankin da su yi biyayya ga dokar kullen su zauna a gidajen su, wacce ta kama aiki nan take inda ya bayyana cewa za a sanar da cikakken ƙarin bayani. Rahoton Punch
Sanarwar na cewa:
"Gwamnatin jihar Kaduna na sanar da sanya dokar kulle a nan take a Sabon Garin Nassarawa-Tirkaniya cikin ƙaramar hukumar Chikun.
"An cimma wannan matakin ne bayan an samu ɓarkewar rikicin dabanci wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu."
“An umurci jami'an tsaro da su tabbatar an bi dokar a yankin da abin ya shaga domin dawo da doka da oda yayin da ake cigaba da bincike. Ana kira ga jama'a da su tabbatar sun bi wannan umurnin wannan dokar wacce ta kama aiki nan take."
Mutum 1 Ya Jikkata Yayin da Magoya Bayan PDP da APC Suka Yi Kaure da Fada a Ribas
A wani labarin na daban kuma, an samu ɓarkewar rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Rikicin ya janyo wani mutum guda ɗaga cikin masu faɗan ya jikkata. Rikicin ya fara ne bayan da magoya bayan PDP suka fara zanga-zanga kan sakamakon zaɓen jihar.
Asali: Legit.ng