‘Ku Bari Na Sauka’: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Rude a Jirgin Najeriya, Ta Gaza Numfashi

‘Ku Bari Na Sauka’: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Rude a Jirgin Najeriya, Ta Gaza Numfashi

  • Wata fasinjan da ta takura a jirgin Airpeace na Najeriya ta tada hankalin jama’a a lokacin da jirgin ke kokarin tashi
  • An ga lokacin da ta bude murya take tsala ihu tare da cewa bata iya numfashi a jirgin, a sarara mata ta sauka
  • Roko da kukan da take bai sa masu aiki a cikin jirgin sun saurare ta ba, sun hana ta sauka duk da ta nemi hakan

Wata ‘yar dirama ta barke a jirgin Airpeace na Najeriya yayin da wata mata ta ke ihun neman ceto kasancewar ta gaza yin numfashi.

Bidiyon da @mr.k.o.b1 ya yada a TikTok ya nuna lokacin da matar ke neman sauka daga jirgin tana cewa ta gaza yin numfashi a cikin jirgin.

Masu aiki a cikin jirgin sun yi biris da ita, inda suka nuna alamar ba za su bari ta sauka daga cikin jirgin ba.

Kara karanta wannan

Kamar bandaki: Gidan da budurwar da ta gaji da biyan haya ta gina ya girgiza intanet

Yadda mata ta rude daga shiga jirgi, ta ba da mamaki
Lokacin damatar ke kuka a cikin jirgin Airpeace | Hoto: @mr.k.o.b1
Asali: TikTok

Wata mata da ke gefe ta shiga rudani, inda ta roki ma’aikatan jirgin da su bari ta sauka tunda tana son hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar da ke kukan ta ce, tana son ba ta dan lokaci ta sauka, amma wani ma’aikaci ya sa hannu ya hana da fita a lokacin da ta tashi tana neman hanya.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Bidiyon dai ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra’ayoyinsu kan halin da matar ta shiga. Ga kadan daga martanin jama’a:

@LAconfidence24:

"Wannan ya taba faruwa dani a lokacin da na shiga wata bas, wancan mutumin ya dauka matar nan wasa take. Kawai tana bukatar shan iska ne na minti daya shikenan za ta dawo daidai.”

@Cameroon football coach:

"Jikinta baya jituwa da jirgin sama ne..tana da gaskiya, ya faru dani a lokacin da na sauya birni.”

Kara karanta wannan

Kaico: An debi 'yan kallo yayin da saurayi ya kama budurwa a otal tana karuwanci

@Altoos:

"Hakan ya taba faruwa dani a irin wannan jirgin, masuburbudar sanyinsu bata da kyau.”

@choice care:

"Jirgin da babu abin da ke aiki a cikinsa kuna son kashe mutum a cikin irin wannan lalataccen jirgin don Allah rayuwar mutum na da daraja.”

@Sarah nwaka:

"Allah ma ya sani da nice zan kafta wa daya daga cikin mazan nan mari mai kyau...ta shake ne tana bukatar iska mai kyau.”

@Immaculate:

"Wa ya sani ko tana da cutar asthma...ba za ku tsammanci mutane su sanya alamar halin lafiyarsu a goshinsu ba.”

@RichardDiva:

"Meye zai kai ku hawa jirgin Airpeace ku ma? Ku tallafawa motocin God is Good mana... yanzu za ta iya yin numfashi.”

Wata budurwa kuwa, kanta ta ginawa gida karami domin huce haushin biyan kudin haya da take yawan yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.