An Kama Mutumin Da Ya Yi Barazanar Gayyatan Yan IPOB Lagas
- Yan sanda sun kama sugaban Inyamurai wanda aka gani a bidiyo yana barazanar gayyatan yan IPOB zuwa Lagas
- Fredrick Nwajagu, Eze Ndigbo na unguwar Ajao da ke jihar Lagas ya yi barazanar a wani bidiyo a yammacin Juma’a
- Wata majiya ta yan sanda ya bayyana cewa ya gudu daga gidan lokacin da yan sanda suka isa wajen a safiyar Asabar amma aka gano shi a wani otel
Lagos - An kama Fredrick Nwajagu, Shugaban Inyamurai na yankin Ajao da ke jihar Lagas.
An gano Nwajagu a wani bidiyo da ya yadu a ranar Juma’a, 31 ga watan Maris, yana barazanar gayyatan mambobin haramtaciyyar Kungiyar IPOB zuwa Lagas da sunan kare kadarorin yan kudu maso gabas, jaridar Punch ta rahoto.
Daily Trust ta nakalto yana cewa:
“Yan IPOB, za mu gayyace su. Basu da aiki. Dukkanin yan IPOB za su kare duk shagunanmu. Kuma ya zama dole mu biya su. Ya zama dole mu kwasi su Don yin haka. Dole mu kasance da tsaronmu don sun daina farmakarmu da tsakar dare, da safe da kuma rana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Idan suka gane cewa Muna da tsaronmu kafin su zo, Za su shiga taitayinsu. Ban fadi wata magana da za a boye ba. Ba zan boye kalamaina ba, a bari kalamaina su shahara. Ya zama dole Inyamurai su samu yanci sannan su samu matsaya a jihar Lagas.”
Wata majiya ta yan sanda ce ta sanar da ci gaban, inda ta bayyana cewa jami’an hadin gwiwa na yan sanda da DSS me suka kama jigon Inyamuran ne a safiyar Asabar.
A cewar majiyar:
“Wata tawaga ta yan sanda da DSS sun je fadarsa amma ya rigada ya gudu. Daga baya aka gano shi a wani Otel a Ejigbo inda aka kama shi.”
Bidiyon yadda masoyin Peter Obi Peter Obi ya haddasa dirama a jirgin sama
A wani labari na daban, mun kawo cewa wani dan Obidient da ke goyon bayan dan takarar Labour Party a zaben shugaban kasa da aka yi, ya haddasa yar dirama a cikin jirgin sama yayin da zai tashi daga Abuja zuwa Lagas.
Mutumin dai ya fasa ihu cewa ba za a rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba domin a cewarsa ba shine ya lashe zabe ba.
Asali: Legit.ng