Sabon Salo: Yadda Butum-Butumi Ya Kaiwa Wani Matashi Da Abinci a Gidan Cin Abinci, Bidiyon Ya Dauka Hankali

Sabon Salo: Yadda Butum-Butumi Ya Kaiwa Wani Matashi Da Abinci a Gidan Cin Abinci, Bidiyon Ya Dauka Hankali

  • Wani bidiyo da ke nuna gidan cin abinci da ya yi amfani da butum-butumi wajen kaiwa dan Najeriya abinci ya yadu a Instagram
  • A bidiyon, an gano butum-butumin yana kaiwa kwastoma da ya cika da farin ciki abinci
  • Mutumin da ya karbi abincinsa daga wajen butum-butumi dauke da murmushi ya yi kokarin rungume na'urar da ta gano inda yake zaune

Wani bidiyon butum-butumi yana kaiwa wani matashi abinci a gidan cin abinci ya haifar da cece-kuce game da wurin aiki a karni na 21.

A bidiyon wanda @tundednut ya wallafa, mutumin ya yi farin cikin karbar abincinsa daga wajen butum-butumi wanda ya iya gano mamallakin abincin ba tare da taimakon wani ba.

Butum-butumi ya kaiwa matashi abinci
Sabon Salo: Yadda Butum-Butumi Ya Kaiwa Wani Matashi Da Abinci a Gidan Cin Abinci, Bidiyon Ya Dauka Hankali Hoto: @tundednut
Asali: UGC

Matashi cike da farin ciki ya karbi abincinsa daga wajen butum-butumi

Bayan ya gabatar masa da abincin, nan take sai butum-butumin ya yi tafiyarsa, kumna mutumin da ya karbi abincin nasa ya kasance cikin mamaki, ya dagawa butum-butumin hannu.

Kara karanta wannan

Kuna ruwa: Bidiyon 'yan mata sun dinke da abinci, suna jiran wacce za ta biya a cikinsu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama da suka ga butum-butumnin sun damu sosai domin alamu sun nuna butum-butumin zai raba mutane da dama da aikinsu.

Hatta mai amfani da Instagram din wanda ya wallafa bidiyon ya yi martani makamancin wannan, yana mai nuna cewa akwai dubban mutane da basu da aiki a Najeriya wadanda za su yi farin cikin yin aikin butum-butumin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@officialmorientez ya ce:

"Ka yi tunani ace ya dauki abincina zuwa wani tebur na daban zai ga hauka."

@ijoba101 ya rubuta:

"Me yasa butum-butumin bai dauki abincin ya daura kan teburin ba tun da hankali ya yi masa yawa."

@yuuriavvuiLCJay ya yi martani:

"Ina tunanin ranar da butum-butumin zai ci mun abincina...za ku san cewa ni Zazoo ne kuma ina zama ne a gidan ZOO."

Matashi ya gwangwaje mahaifiyarsa da dankareren gida a bidiyo

Kara karanta wannan

“Duk Naki Ne Uwata”: Matashi Ya Kerawa Mahaifiyarsa Hadadden Gida, Bidiyon Ya Dauki Hankali

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya kerawa mahaifiyarsa wani katafaren gida mai kama da aljannar duniya wanda ke dauke da dakunan bacci har guda biyar.

Matashin ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta cancanci komai a wajensa don haka ya yi mata wannan babban kyauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng