Gwamnan PDP Ya Kori Dukkan Hadimansa Bayan Shan Kaye A Zabe
- Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ya sallami dukkan masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa
- Hakan na zuwa ne bayan Ikpeazu ya sha kaye a takarar neman kujerar sanata kuma wanda ya so ya gaje shi ya zama gwamnan jihar shima ya sha kaye
- Gwamna Ikpeazu ya yi godiya ga hadimansa da ya sallama ya kuma musu fatan alheri a duk wani aiki da za su yi a gaba
Jihar Abia - Gwamnan Jihar Abia da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya, Okezie Ikpeazu ya amince da korar dukkan masu mukaman siyasa a jihar, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Sakataren gwamnatin jihar Anambra, Barrister Chris Ezem ne ya fitar da sanarwar korar masu mukaman siyasan.
Rukunin wadanda Gwamna Ikpeazu ya sallama daga aiki
Wadanda abin ya shafa sun hada da: Mataimaka na musamman, Manyan mataimaka na musamman, Mashawarta na musamman da jami'ai na fasaha.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan kari ne bisa masu mukaman siyasa da gwamnan ya kora bayan ya gaza yin nasarar cin zabe don zuwa majalisar dattawa kuma wanda ya so ya gaje shi ya sha kaye a zaben gwamna.
Ikpeazu ya umurci Akanta Janar ya biya wadanda aka kora albashin Maris
Gwamnan ya kuma umurci Akanta Janar na jihar ya tabbatar an biya albashin watan Maris ga dukkan masu mukaman siyasan da aka kora nan take.
Gwamnan ya musu godiya bisa gudunmawar da suka bada da ayyukansu ga jihar sannan ya musu fatan alheri a ayyukan da za su yi a gaba.
Gwamna Ikpeazu ya sallami surukinsa daga aiki, ya ce kwamishina ya maye gurbinsa
A wani rahoton a baya, Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya kori surukinsa, Rowland Nwakanma, mataimakin shugaban, Hukumar Kare Muhalli na Jihar Abia, ASEPA, reshen Aba daga aiki.
An bayyana hakan ne cikin wata takarda da Barista Chris Ezem, sakataren gwamnatin jihar Abia, ya fitar wacce ta ce an 'kori dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli na Aba sai dai banda na Ikot Ekpene da Express, da Aba-Owerri Road.'
Ikpeazu ya bada umurnin cewa kwamishinan muhalli na jihar Abia, Mr Sam Nwogu ya maye gurbin shugaban da aka sallama.
Asali: Legit.ng