Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Bude Shafin Intanet Don Dattijai Wadanda Suka Yi Ritaya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Bude Shafin Intanet Don Dattijai Wadanda Suka Yi Ritaya

  • Cibiyar Kula da Dattijai na Kasa, NSCC, za ta kirkiri wani shafin intanet don sada dattijai wadanda suka yi murabus daga aiki da wasu ayyukan
  • Shugaban NSCC, Dakta Emem Omakaro ta ce dattawan Najeriya na da kwarewa da basira da za a ai iya amfana da shi a wasu bangarori ba sai aikin gwamnati ba
  • Omakaro ta ce wannan shafin na intanet da zai fara aiki a watan Afrilun 2023, zai rika za ta dattijan da ayyuka ta yadda za su cigaba da bada gudumawa ga cigaban kasa

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta kirkiri shafin intanet da nufin zaburarwa da sake amfana da dattawa da ke son cigaba da yin aiki bayan yin murabus, Daily Trust ta rahoto.

Dakta Emem Omakaro, Shugaban Cibiyar Kula Da Dattijai na Kasa, NSCC, ta bayyana hakan yayin wani taron hadin gwiwa tare da hukumomin gwamnati da abin ya shafa da masu ruwa da tsaki a kan batun a Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

Omakaro
Gwamnatin Najeriya Za Ta Bude Shafin Intanet Don Dattawa. Hoto: Stallion Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron mai lakabin 'NSCC Continuing Engagement Bureau Programme' an shirya shi don don kulla zumunci tsakanin cibiyar da abokan huldarta

Dalilin bude wannan shafin na intanet - Omakaro

Omakaro ta ce an dauki wannan matakin ne bayan gano babban amfani da za a samu daga dattawa domin cigaban kasa.

Ta ce:

"Manufar hagin gwiwar kuma ita ce a taimaka wa cibiyar don ƙirƙirar shafin intanet wacce za ta bawa dattawa waɗanda ƙwararru ne a bangarori daban-daban su yi amfani da kwarewarsu.
"Wannan taro ne masu bada gudunmawa da ayyukan cigbaba, cigaba da aikin na nufin mun katsa ritayarsu.
"Za mu kirkiri dandali da kayan aiki, muna samar da gurabe don dattawa da ke son cigaba da aiki kuma su samu daman yin hakan."

Ta cigaba da cewa:

"Ka san, dattawa na da daman cigaba da bada gudunmawa a kowanne bangare idan sun so kuma suna da damar samun aiki bayan murabus ba dole sai gwamnati ta basu aiki ba.

Kara karanta wannan

IPAC Ta Yi Martani Yayin da DSS Ta Gano Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi

"Mun yi imanin cewa tsofaffi na da basira da baiwa da kwarewa don haka za mu iya amfana da kwarewarsu.
"Mun gina shafin mu na intanet saboda muna bukatar dukkan bayanai da ya kamata mu samu, daga aikin gwamnatin tarayya, jiha ko karamar hukuma ka yi ritaya."

Shugaban hukumar ta ce za a bude shafin na intanet a watan Afrilu kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Gwamnan Abia ya kore surikinsa daga aiki

A wani rahoto, Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya sallami surikinsa, Rowland Nwakanma, mataimakin shugaban, Hukumar Kare Muhalli na Jihar Abia, ASEPA, reshen Aba daga aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164