Gobara Ta Sake Tashi a Jihar Legas, Ta Laƙume Shaguna Da Dama
Wata mummunar gobara ta sake tashi a wata babbar kasuwar sayar da kayayyaki a jihar Legas
Mummunar gobarar wacce ba sa tushen ta ba tayi silar asarar kayayyaki na miliyoyin naira
Gobarar itace ta biyu da ta tashi cikin ƴan kwanaki kaɗan cikin wasu manyan kasuwanni a jihar Legas
Jihar Legas- Wata mummunar wuta ta kama a wata babbar kasuwar siyar da safaya part a jihar Legas.
Wutar ta kama ne a kasuwar 'spare part' ta Olowo a jihar Legas da safiyar ranar Alhamis. Rahoton Vanguard
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Daily Post ta samo cewa wasu daga cikin shagunan da mutar ta kama a ciki suna ɗauke da kayayyakin AC, kayan ababen hawa, kayan babura da sauran su.
Ƴan kasuwar sun tafka asarar kayayyaki na miliyoyin naira a dalilin tashin gobarar wacce ba a san maƙasudin abinda ya haddasa tashin ta ba.
Jami'an hukumar ƴan kwana-kwana na jihar Legas da jami'an tsaro sun garzaya inda lamarin ya auku a kasuwar domin shawo kan gobarar.
Idan ba a manta ba a cikin ƴan kwanakin da suka wuce, an kuma samu irin wannan gobarar a kasuwar Akere ta 'spare parts' wacce ke kan titin hanyar Kirikiri, Olodi-Apapa a yankin Ajegunle na jihar Legas.
Ana yawan samun tashin gobara a kasuwanni daban-daban na ƙasar nan. Ƴan kasuwa da dama na kwana a ciki idan aka samu tashin gobara saboda asarar da suka tafkawa ta miliyoyin naira.
Mummunan Gobara Ta Tashi A Fitacciyar Kasuwa A Legas, Bidiyo Ya Fito
A wani labarin na daban kuma, wata gobara ta tashi a jihar Legas cikin wata fitacciyar kasuwa da ake hada-hadar kasuwancin miliyoyin naira a cikin ta.
Gobarar dai ta tashi ne a wurare daban-daban na kasuwar inda kayayyaki na miliyoyin naira suka salwanta. Ƴan kasuwa da dama ta ritsa da su a gobarar inda suka yi asara matuƙa.
Gobarar ta auku ne a fitacciyar kasuwar nan wacce ta shahara a jihar Legas, kasuwar Balogun, a ranar Talatan da ta gabata wato ranar ashirin da takwas ga matan Maris na shekarar dubu biyu da ashirin da uku (2023) miladiya.
Asali: Legit.ng