Bankuna Sun Shiga Damuwa Saboda Mutane Basa Zuwa Ajiye Kuɗi
- Bankuna sun shiga halin tsilla tsilla tun da aka sanar da dokar canja fasalin kuɗi da amfani dasu
- Mutane sun rasa kuɗin kashewa, wanda hakan yasa ko sun samu kuɗi basa iya zuwa banki su ajiye
- Hattana yan boko da ƴan zamani, yanzu gudun bankuna suke idan sun samu cash, hakan ya tayar wa da bankuna hankali
Damuwa tayi yawa a zuƙatan bankunan kasuwanci a Najeriya.
Wani ma'aikacin banki ya tabbatar da cewar, mutane sun hasala, yanzu takai ta kawo har sun cire sha'awar da suke ta ita na zuwa amsa ko ajiye tsabar kuɗi a banki.
Wannan ya samo asali ne sakamakon kaddamar da tsarin nan na canja fasalin Naira, wanda hakan yasa ƴan Najeriya da yawa suka fidda rai da amfani da tsarin banki.
Ma'aikacin bankin ya shaidawa jaridar The Nation cewar:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ba abu bane mai kyau idan ba'a zuwa amsar tsabar kuɗi a banki, ta wajen wajen amsar kudi ko ta Manhajar bankuna."
Ya ƙara da cewa:
"Hakan na nufin dole ne a duba tsarin samar da kuɗin zuwa yanayi mafi kyau wanda hakan zai shafi bada lamuni".
Babban ma'aikacin bankin yace, rasa sha'awa da mutane suka yi da bankuna, yasa yanzu basa dawo da tsabar kuɗi dake a hannun su.
Wanda ya alaƙanta mutane nayin haka ne saboda tsoron da suke dashi na cigaba da dulmiya cikin tafkin rashin kuɗi tsaba.
Ya ƙara da cewa:
“Masu fafutukar neman kuɗi waɗanda ba yan gargajiya ba, suma sun jibge tsabar kudi a gida, kuma a lokaci guda, idan zasu sake kuɗin dake hannun su, zasu zamto sun wadata ba'a hannun mutane ba kawai, har cikin bankuna". inji shi.
Ma'aikacin bankin daya nemi a sakaya sunan sa yace rashin isassun kuɗaɗe na daya da cikin halin zulumi dake damun bankuna sakamakon dokar kayyade yawan kudi da CBN ta kawo.
Amma ya ƙara bayyana kwarin gwuiwar sa akan sake saye zuciyar mutane akan harka da banki.
Inda daga karshe ya bada shawarar yadda lamarin zai inganta ta hanyar:
"Kara kaimi daga CBN akan samar da ƙudi isassu, wanda suka haɗa da sababbi da tsofaffi, inda yace tabbas idan akayi haka, za'a sake saye zuciyar mutane akan harka da banki".
CBN ya saki sunan Bankuna guda 10 da zasu iya bada POS
A wani rahoton mai kama da wannan babban bankin Najeriya ya saki sunayen bankuna guda 10 da basu da banki na zahiri amma zasu iya bada POS.
Bankunan kawai suna a manhaja ne amma suna bin dokoki iri daya ne da bankunan gargajiya.
Asali: Legit.ng