CBN ta Saki Sunayen Bankuna 10 Dake da Lasisin Bada POS Kuma Yayi Aiki a Matsayin Bankin Kan Waya

CBN ta Saki Sunayen Bankuna 10 Dake da Lasisin Bada POS Kuma Yayi Aiki a Matsayin Bankin Kan Waya

 • Babban bankin na Najeriya yace bankuna 10 kawai ya bawa lasisin aiki matsayin bankunan kan waya
 • Babban bankin yace, bankunan kuma zasu iya aiki a matsayin ƙaramin bankin bada lamuni ga ƙananan sana'o'i a ƙasa
 • Bankin yace, bankunan basu da ofisoshi da yawa kamar sauran bankuna, sai dai suna da manhajojin su, kuma duk doka ɗaya suke amfani da ita da sauran bankunan gargajiya

Bankunan da ake amfani dasu a waya na cigaba da samun haɓaka a Najeriya, saboda yadda masu bankunan ke ci gaba da samar da kayan fasaha na zamani da suke warware matsalolin ƴan Najeriya wajen amsa da aika ƙudi.

Domin a tabbatarwa a wannan ƙarni ba'a bar kowa a baya a harkar kuɗi na zamani ba, CBN ya bawa kamfanoni damar buɗe bankuna masu amfani da manhaja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bam Ya Tashi Da Babban Mai Hada Bama-Bamai Na Ƙungiyar Boko Haram

Saidai bankunan da suke ƙanana marasa reshe yanzu haka zasu iya bada POS da kuma duk wata harkar kuɗi kamar yadda aka saba a bankunan gargajiya na yau da gobe.

CBN Bank
CBN ta Saki Sunayen Bankuna 10 Dake da Lasisin Bada POS Kuma Yayi Aiki a Matsayin Bankin Kan Waya Hoto: Legit.ng
Asali: Facebook

Kananan Bankunan Kan Waya Yana Shafe Bankunan Gargajiya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da cewa a kan manhajoji suke kawai, waɗannan bankuna nakan waya na cigaba da shafe bankuna na gargajiya saboda yadda suke warware matsalolin Najeriya cikin ƙiftawar ido.

Bankunan ana musu iƙirari da "Fintech" a turance, kuma suna cikin jerin "Muhallin Bankuna Masu hada-hadar kuɗi ta hanyar amfani da fasaha", suma aikin su ɗaya da bankunan gargajiya.

Wani rahoto ya nuna cewa, irin waɗannan bankuna suna aikine a ƙarƙashin wasu tarin lasisi daga wurare daban daban, wanda suke samar da ayyukan kuɗi cikin sauƙi da kuma aiki akan manhajar waya da wuraren kasuwanci a kasuwanni, shaguna da sauransu.

Kara karanta wannan

CBN Na Shirin Dakatar da Ayyukan Bankuna 2 a Najeriya Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

Kamar yadda kundin tattara bayanai na CBN ya zayyana, a ƙalla kamfanunnuka

894 aka bawa lasisi su zama ƙananan bankuna na kusa da talaka zuwa Fabrairu, 2023.

Amma kaɗan daga cikin tarin waɗannan bankuna ne aka bawa damar zama bankunan kan waya masu aiki a manhajar waya da zasu iya bada na'urar POS.

A cikin bankunan kan wayar dake amfani da manhajar waya, kaɗan ne suka samu lasisin soma bada na'urar POS daga CBN.

Ga jerin waɗannan bankuna a ƙasa kamar yadda Legit.ng ta ruwaito :

 • Sofri
 • Mint
 • Piggyvest
 • VFD
 • Moniepoint
 • FairMoney
 • Carbon
 • Kuda
 • Eyowo
 • Sparkle

Yan Najeriya sun yabi CBN da Bankuna saboda Yadda Bankuna suke ci gaba da Fitar da kuɗi Tsaba.

Yan Najeriya sunji daɗin yadda CBN da Bankuna suke aiki tukuru wajen rage rashin kuɗi, dalili da yasa suka yabi bankunan saboda wadatuwar kudi.

Kara karanta wannan

Bankuna 5: Dukkan abubuwan da ya kamata ku sani game game da bankun Muslunci a Najeriya

A cewar su, an samu canji sosai a kan yadda kuɗi ke zagaya wa yanzu idan aka hada da yadda yake a baya.

Haka yasa masu POS suka koma cajar kaso 6 cikin ɗari na abinda ka cire a maimakon baya da suke cajar kaso 30 a cikin dari na abinda mutum ya cire saboda matsalar karancin kudin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar

Online view pixel