Zabe ya Wuce: Mun Cire Tallafin Kudin Motar Da Muka Sanya – Gwamnatin Lagos
- Bikin zabe ya wuce, talakawa a Legas sun soma girban sakamakon zaben su akan cire tallafin motocin Bas
- Gwamnatin jihar Legos ta cire kaso 50 a cikin dari na kudin bas bas dake tashi a Legos domin rage radadin rashin “Cash”
- Amma yanzu bayan zabe, gwamnatin tace, “Wane Mutum” Bazata iya ba, ta canje tallafin
Lagos - Gwamnatin jihar Legas ta sanar da wani batu daya girgiza mutanen jihar.
Biyo bayan sanarwar data saki cewar, kudin motocin nan na bas bas zasu koma kamar yadda suke kafin wannan lokaci farawa daga 1 ga watan Afrilu mai kamawa.
Idan za’a iya tunawa dai, a watan fabrairu ne Gwamnan jihar Lagos karskashin jagorancin Babajide Sanwo-Olu ta sanar da rage kaso 50 a cikin dari na duk wani kudi da ake biya na bas din mota mallakin gwamnatin jihar Lagos. Rahoton The Cable.ng
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan a wancan lokacin yace, an dauki wannan mataki ne ba don komai ba, sai don rage radadin rashin kudi da man fetur da yayi katutu a wajen mutane.
Shidai ragewa motocin bas bas din kudi da gwamnatin jihar ta Legas tayi, itace daitayi tun gabanin zaben gwamnoni da akayi a watan Maris 18.
Gwamnatin data sanya ta cire tallafin ita INEC ta ayyana a matsayin wadanda sukayi nasara a zaben.
Jaridar Sahara reporters ta ruwaito bayani daga gwamnatin jihar, ta hannun hukumar dake kula da zirga zirgan bas bas din a cikin garin Lagos, LAMATA.
A cewar bayanin kamar yadda Channelstv ta sanya:
“Daga ranar 1 ga watan Afrilu, duk kudin bas bas na gwamnati za’a koma biya dari bisa dari.” Inji LAMATA.
“Duba da cigaba da aka samu tsakanin Kotun koli da Gwamnatin tarayya akan dawo da tsofaffin kudi hade da sababbin, wanda haka ya dawo da yanayi mai kyau na rashin kudi, ragin kaso hamsin a cikin kudin mun tsaida shi daga 1 ga watan Afrilu.”
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
Zulum Zai Gina Gidaje 20, 000 ga Yan Gudun Hijra
Labari mai dadi daga jihar Borno da jaridar Legit.ng ta ruwaito na nuna yadda Gwamnan jihar Borno zai sake gidanawa yan gudun hijra gidaje 20,000.
Za’a raba gidajen ne a kauyuka uku domin sake tsugunar da bayin Allah da yakin Boko haram tilastawa zuwa gudun hijra kasar Chadi, Kamaru da Nijer.
Asali: Legit.ng