Matashi Ya Dasa Gini, Ya Dauki Malaminsa Don Ya Sanya Albarka, Gidan Ya Kammalu a Kan Lokaci
- Wani matashi dan Najeriya wanda ya kammala ginin gidansa ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda abun ya fara
- A wajen aza harsashin gidan, an gayyato wani malamin addini domin ya yi addu'a tare da sanya tabarraki a gidan
- Abun ya burge masu amfani da TikTok da dama da suka ga yadda cikin ginin ya hadu bayan kammala shi
Wani matashi dan Najeriya (@alexmikano8) ya cimma babban nasara a rayuwarsa yayin da ya fara da kuma kammala wani hadadden ginin gida.
Lokacin da aka aza harsashin gidan, mutumin ya fawwalawa Allah komai sannan ya gayyaci wani malamin addini domin ya sanya albarka a kan aikin gidan.
Matashi ya yi fentin gidansa da kaloli masu kyau
Wani bidiyo da ya wallafa ya nuno yadda aka fara ginin a mataki mabanbanta. Lokacin da aka yi ginin, ya kashe makudan kudade wajen kawata cikin gidan zuwa na zamani. wajen gidan ma ya hadu sosai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyonsa sun tayua shi murnar cimma wannan nasara a rayuwarsa yayin da wasu suka yi addu'an Allah ya yi masu irin wannan ni'imar.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@MAKANAKI ya ce:
"Ina tayaka murna danuwa."
@userjoeya ce:
"Ina tayaka murna babban yaya."
@Emmanuel Goodlife1 ya ce:
"Ina tayaka murna. Allah ya mu irin taka."
@Favy ya ce:
"Allah ya yi mun irin wannan ni'imar."
@kaimachukwuwisdom ya ce:
"Ina tayaka murna. Ina neman irin ya taka."
@Pavel ya ce:
"Mutumina dan Allah ka hada ni da injiniyan da ya yi maka wannan."
@Oma ya ce:
"Ina tayaka murna....Allah ya yi ma dan uwana irin wannan."
@V.O.N ya ce:
"Allah ya kara ni'ima mai gida na ji karfin gwiwa."
Bidiyon yadda kare ya kula da uwar dakinsa yayin rashin lafiya ya dauka hankali
A wani labari na daban, mun ji cewa wani kare ya dauka hankalin jama'a bayan bayyana bidiyonsa yana taya uwar dakinsa aikace-aikacen gida yayin da take rashin lafiya.
An dai gano karen dauke da butan karfe inda ya je famfo ya debo ruwa sannan kuma ya daura a kan rishon girki mai aiki da lantarki.
Asali: Legit.ng