Gwamnati a Ƙarƙashin Jagorancin Tinubu Zata Kasance Mai Tasiri ga Rayuwar Ƴan Najeriya – Buhari
- Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace ko shakka bayayi Bola Ahmed Tinubu, zai kafa gwamnati mai tasiri
- Shugaban ya aike da wannan sakon ne ta hannun mai taimaka masa a kafafen yaɗa labarai, Femi Adesina
- Buhari ya kuma taya Bola Tinubu Tinubu murnar cika shekaru 71 a duniya
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da ƴan Najeriya cewar, gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu zata gudanar da mulki mai tasiri.
Buhari yace Gwamnatin Tinubu zata taɓa kowanne ɓangare na rayuwar ƴan Najeriya da zarar ya amshi mulki daga hannun sa.
Shugaban ƙasar ya bada wannan tabbacin ne a ranar Talatar nan a wani saƙo daya fitar ta hannun mai taimaka masa a kafafen yaɗa labarai, Femi Adesina.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Buhari, Najeriya zata samu gwamnati mai tasiri a ƙarƙashin jagorancin Tinubu.
Ya tabbatar da cewar, Tinubu yana da kwarewar siyasa da kuma ilmi da zai sanya ya kafa gwamnati mai tasiri da zarar ya amshi mulki a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.
Buhari yace ta hannun Femi Adesina:
"A matsayin sa (Tinubu) na zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da zai karɓi mulki yana da shekaru 71, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana da tabbacin kwarewarsa a fagen siyasa tun daga 1999,"
Jaridar vanguard tace Buhari ya ƙara da faɗin:
"Yana da ƙwarewa a siyasar jam'iyya, tunda har an zaɓen Sa'a matsayin sanata, kuma ya shiga cikin tsarin shugabancin majalisa shekaru masu yawa. Wannan ƙwarewa zata zamto masa kadara wajen samun gwamnati mai tasiri".
"Shugaba Buhari ya yarda da cewa, iya zama da mutane na Asiwaju, da kyautatawa shine zai zama jagora wajen janyo kwararru daga ciki da wajen ƙasar da zai zama ummul-aba-isin sanya tattalin arziki na ƙasar ta samu cigaba mai ɗorewa...".
"Na Sama Da Mu Sun Karbi Tuhumar", 'Yan Sanda Sun Bayyana Halin Da Ake Ciki Game Da Shari'ar Ado Doguwa
Daga karshe Buhari ya taya murna ga sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, abisa zagayowar ranar haihuwar sa, bayan Tinubu ya cika shekaru 71 a duniya.
Femi Adesina ya ƙarkare da cewarsu:
"Shugaba Buhari yana addu'ar Allah ya bawa Asiwaju Tinubu da iyalinsa lafiya". Inji sakon.
Abin Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Fara Yi Inji Festus Keyamo
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya naci gaba da samun shawara daga lungu da saƙo na ƙasa.
Festus Keyamo ya hori Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, daya daure ga wanzar da alƙawurran yaƙin neman zaɓen sa ana rantsar dashi.
Barista Festus Keyamo (SAN) ne yayi wannan roƙo, inda idan har Tinubu nasonua saye zuciyar ƴan Najeriya. Wannan ita ce hanyar sambeɗar da zai iya yin hakan.
Asali: Legit.ng