Ana Dab Da Yayi Bankwana Da Mulki, An Bukaci Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Wata Muhimmiyar Doka
- An buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya rattaɓa hannun kan ƙudirin dokar kafa hukumar ƴan bijilanti kafin ya bar ofis
- Babban kwamandan ƙungiyar na ƙasa shine yayi wannan kiran ga shugaban ƙasar a birnin Abeokuta
- Babban kwamandan ya bayyana cewa sanya hannu kan ƙudirin dokar kafa hukumar ba ƙaramin tagomashi zai kawowa tsaron ƙasar nan ba
Jihar Ogun- Ƙungiyar ƴan sakai ta Najeriya tayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar ƴan sakai kafin zuwan ranar 29 ga watan Mayu lokacin da zai bar kan karagar mulki.
A cewar ƙungiyar, majalisar tarayya tuni ta amince da kuɗirin kafa hukumar na VGN (Establishment) Bill 2022. Rahoton Punch
Babban kwamandan ƴan sakan, Dr Usman Jahun, shine ya bayyana hakan a birnin Abeokuta, jihar Ogun yayin tattaunawa da ƴan jarida lokacin da ya kai ziyara kan ƴaƴan ƙungiyar a yankin Kudu maso Yamma.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Majalisar wakilai da majalisar dattawa duk sun amince da ƙudirin dokar. Abinda kawai muke jira shine sa hannun shugaban ƙasa."
"Saƙon mu ga shugaban ƙasa shine kafin ya bar karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, muna roƙon sa da ya rattaɓa hannun kan wannan ƙudirin dokar domin ƴan Najeriya su cigaba da samun zaman lafiya da tsaro a ƙasar."
Jahun ya bayyana cewa amincewa da ƙungiyar a hukumance zai samar da ayyukan yi sannan zai sanya jami'an ƴan sakai su cike giɓin rashin isassun jami'an tsaron da ake fama da su a ƙasar nan. Rahoton Daily Trust
“A mafi yawa daga cikin ƙauyukan mu, akwai giɓi sosai. Sannan akwai buƙatar a cike dukkanin waɗannan guraben a cikin ƙauyukan mu." Inji shi
"Saboda haka, muna kira ga gwamnati da ta rattaɓa hannun kan wannan ƙudirin dokar domin mu cike wannan giɓin."
Kungiyar CAN Ta Janyo Hankalin Al'ummar Jihar Adamawa Game Da Zaben Cike Gurbi
A wani labarin na daban kuma, ƙungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Adamawa, tayi wani muhimmin kira ga al'ummar jihar.
Ƙungiyar ta janyo hankulan su kan abinda yakamata su yi a zaɓen cike gurbi na gwamnan jihar dake tafe.
Asali: Legit.ng