Mercy Aigbe Ta Magantu Kan Gwagwarmayar Da Matan Musulmi Ke Yi a Ramadan

Mercy Aigbe Ta Magantu Kan Gwagwarmayar Da Matan Musulmi Ke Yi a Ramadan

  • Jarumar Nollywood Mercy Aigbe ta yi korafi game da kalubale da wahalhalun da matan Musulmi kan fuskanta a lokacin azumin Ramadan
  • Jarumar fim din ta wallafa wani hotonta tana gyangyadi tare da bayyana yadda take fama da tashin sahur
  • Mercy ta yi karin haske cewa yayin da take fama da azumi, tana kuma shan wahala wajen shirya abincin sahur

Shahararriyar jarumar Nollywood Mercy Aigbe ta koka game da wahalhalun da matan Musulmi kan fuskanta a lokacin azumin Ramadana.

Mercy ta wallafa hotonta tana gyangyadi sannan ta bayyana wahalar da ke cikin tashin sahur.

Jarumar fim tare da mijinta
“Ai Kirista Ce Ke”: Mercy Aigbe Ta Magantu Kan Gwagwarmayar Da Matan Musulmi Ke Yi a Ramadan Hoto: @realmercyaigbe
Asali: Instagram

Jarumar fim din ta yi karin haske cewa yayin da take fama da azumi, tana kuma fuskantar matsala wajen tashi cin sahur saboda rashin isasshen bacci na gajiyar da ita.

Mercy Aigbe ta caccaki mijinta, Kazim Adeoti, kan wallafa hotonta a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Toh fa: Mutumin da ya ba da maniyyinsa aka haifi yara sama da 500 zai fuskanci tuhumar kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalamanta:

"Toh ku dukkanku da kuke cewa mijina na da saukin kai, kun ga abun da ya yi mani ko da sanyin safiyar nan.
"Tashin yin sahur ba abu ne mai sauki ba!!! Na fara sabawa sosai da azumi, amma kun ga tashi girkin nan da cin abincin asussubahin nan, gwagwarmaya ne da bacci ba zai barni ba
"Allah madaukakin sarki ya amshi sadaukarwarmu a matsayin ibadah, ya yafe mana kura-kuranmu sannan ya amsa mana dukkan bukatunmu, ya ci gaba da yi mana albarka da saka mana da kyawawan ayyuka."

Ga wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

officiallyndam:

"Ke musulma ce yanzu? Na zata ke kirista ce a baya? Aure ya sauya addinin. Abu ya yi kyau. Ina maki fatan alkhairi a azumin ki."

sandraashionyeuzuh:

"Ke kirista ce ko musulma?"

nuriyahtraveltour:

"Allah madaukakin sarki zai amsa mana a matsayin ibadah inshaallah ❤️ kada ki damu za ki sama da hakan.❤️"

Kara karanta wannan

"Matan Najeriya Kaso 77% Dake Bilicin, Duk Suna Fuskantar Hadarin Sankarar Mama" NAFDAC

Legit.ng ta tuntubi wasu matan aure don jin ya suke gudanar da harkokin gida a wannan wata na Ramada.

Khadija Muhammad ta ce:

“Gaskiya abun sai sam barka, shekaruna 6 da aure kenan kuma Alhamdulillah ina iya bakin kokarina wajen sauke hakokin da suka rataya a wuyana a matsayina na uwargida musamman a wannan wata na Ramadana.
“Na kan tsara komai da nake son cimma bisa lokaci kama daga ayyukan gida, lokacin shirya abinci, shirya yara makaranta da kuma girki. Sai dai fa baccin safiyar nan shine babban matsalata da zaran ka kammala sallan asubahi ba za ka samu ka dan koma bacci ba har sai yara sun tafi makaranta. Godiyan ma a sati mai zuwa za su tafi hutu.”

A bangarenta, Zainab kuma cewa ta yi:

“Azumina na farko kenan a gidan miji, gaskiya abun ba sauki na saba a gida muna da yawa kowacce da aikinta amma a nan sai a hankali barin ma tulin wanke-wanken nan bayan an sha ruwa yana ci mun kwarya a tuwo. Kuma fa a gida ban cika damuwa da tashin sahur ba amma yanzu dole na tashi ko don girkawa maigida abun da zai ci. Allah dai ya saka mana mu mata da alkhairi.”

Kara karanta wannan

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta kushe girkin uwar mijinta inda ta ce sam abincin ko dadi bai da shi.

Matashiyar dai ta ce wa surukar tata miyan da ta girka bai da dandano mai kyau domin a cewarta ta zuba gishiri ya zarta a ciki, sai dai matar ta kalle ta ne kawai dauke da murmushi a fuskarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng