Hukumar EFCC Na Bincikar Wasu Ministiri 2 Kan Badakalar Kuɗi

Hukumar EFCC Na Bincikar Wasu Ministiri 2 Kan Badakalar Kuɗi

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta bankaɗo wata badaƙalar biliyoyin naira a wasu ministiri biyu
  • Shugaban hukumar yace yanzu hakan suna nan suna bincikar waɗannan ministirin inda aka tafka wannan aika-aika
  • Abdulrasheed Bawa yace ɗaya daga cikin su anyi badaƙalar kuɗin kwangiloli a cikin ta ya kai na biliyan 4 (N4bn)

Abuja- Hukumar yaƙi da cin hanci da rawa ta ƙasa (EFCC) ta bayyana cewa yanzu haka tana kan binciken wasu ministiri guda biyu inda aka biya kuɗaɗen kwangiloli iri ɗaya har sau biyu. Rahoton Daily Trust

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ministirin na da hannu wajen badaƙalar kwangiloli 20 waɗanda kuɗin su ya kai naira biliyan 4 (N4bn).

Abdulrasheed
Hukumar EFCC Na Bincikar Wasu Ministiri 2 Kan Badakalar Kuɗi Hoto: NewswireNGR
Asali: UGC

Abdulrasheed Bawa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a ofishin sa na hedikwatar hukumar a yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Naɗa Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki

Sai dai shugaban hukumar ta EFCC, bai bayyana sunayen ministirin da lamarin ya shafa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

“Yanzu haka, muna binciken wasu ministiri biyu inda aka biyu kuɗaɗe sau biyu. Kuɗaɗen da aka biya idan aka tara su sun kai na kwangiloli 20 waɗanda kuɗin su ya kai biliyan 4 (N4bn).
"Waɗannan kwangiloli ne waɗanda aka yi su tun shekarar 2018, sannan kuma wasu tsirarun mutane masu saurin ido suka sake zuwa da su."
"Sun cire takardun daga fayil ɗin, suka ƙirƙiri na bogi, sannan tabbas tare da haɗin bakin wasu ma'aikatan gwamnati suka ƙara kuɗin sannan aka biya. Ta yaya hakan zai faru idan muna da hanyoyin biyan kuɗi na zamani?"

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

Kara karanta wannan

Karancin-Kudi: Kungiyar Kwadago Ta Umarci Ma'aikatan Najeriya Su Soma zanga-Zanga Daga Litinin

A wani labarin na daban kuma, hukumar EFCC ta shirya tsaf domin yin ram da wasu gwamnonin jihohi da zarar wa'adin mulkin su ya cika.

Hukumar ta bayyana cewa dukkanin shirye-shiryen da ake buƙata ta kammala su domin tasa ƙeyar waɗannan gwamnonin suna yin bankwana da kujerun su na mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng