Kotun Daukaka Kara Zata Zartar Da Hukunci Kan Shari'ar Gwamnan Jihar Osun
- Kotun dauƙaƙa ƙara ta shirya tsaf domin yanke hukuncin kan wanene sahihin gwamnan jihar Osun
- Gwamnan jihar Ademola Adeleke ya garzaya gaban kotun bayan wata kotu ta soke zaɓen da aka yi masa
- Tsohon gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, yayi nasara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar
Jihar Osun- Kotun ɗaukaka ƙara ta sanya yau a matsayin ranar da zata yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, yayi kan zaɓen gwamnan jihar. Rahoton Daily Trust
Kotun mai alƙalai uku wacce mai shari'a Mohammed Lawal Shuaibu, ke jagoranta tun da farko ta tanadi hukuncin bayaaan ta saurari bayanan lauyoyin gwamna Adeleke da na tsohon gwamna Gboyega Oyetola.
Alƙalan na kotun ɗaukaka ƙarar sun gayawa ɓangarorin biyu cewa sun shirya sauraron ƙarar, saboda wa'adin kwana 60 na sauraron ƙarar bisa tanadin kundin tsarin mulki ya kusa cika.
Gwamna Adeleke dai ya ɗaukaka ƙara ne kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe kan gwamnan Osun ta yanke inda ta soke zaɓen shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kotun tayi hukunci ne wanda ya goyi bayan zargin da Oyetola yake yi inda tace ya tabbatar da zargin da yake yi na yin aringizon ƙuri'u a wasu rumfunan zaɓe.
Adelele ya ɗaukaka ƙara inda ya shigar da ƙorafe-ƙorafe 31, yana neman kotun ɗaukaka ƙarar da ta warware gabaɗaya hukuncin da waccen kotun tayi.
A ɗaya daga cikin dalilin sa na ɗaukaka ƙara, Adeleke yayi jayayya kan cewa kotun ta nuna masa wariya ta hanyar nuni da ɗabi'ar sa ta son tiƙar rawa.
Jaridar Punch ta rahoto cewa rundunar civil defence ta girke jami'an ta a wurare masu muhimmanci a jihar yayin da ake dakun jiran hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar.
Atiku Ya Garzaya Kotu, Ya Lissafo Hanyoyi 12 Da INEC Ta Taimaki Tinubu Ya Kayar Da Shi
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar shugaban ƙasar da ya sha kaye a.hannun Bola Tinubu ya garzaya kotu yana ƙalubalantar nasarar da aka yi a ƙansa.
Atiku Abubakar wanda yayi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yana ƙalubalantar nasarar da Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu a kan sa a zaɓen.
Atiku Abubkar ya lissafo hanyoyi 12 da INEC ta taimaka Tinubu ya kayar da shi.
Asali: Legit.ng