An Kaiwa INEC Hari A Manhajar ta Tattara Bayanai Kimanin 3,834,244 a Zaɓukan Gwamnoni Kaɗai-Pantami
- Najeriya ta ɗauki fasahar zamani ta IREV domin tura sakamakon zaɓukan ƙasar. Sannan ya basu damar bibiyan yadda zaben yake wakana kamar yadda aka gani a zaɓukan da suka gabata.
- Sai dai lamarin yaso yabar baya da ƙura, domin kimanin haraharen yan kutse 3,834,244 aka samu daga ciki da wajen Najeriya
- Ministan sadarwa yace, a ranar juma'a ta jajibarin zaɓe ankai hari akan fasahar ta IREV ta INEC sau 1,046,896, ranar zaɓen kuma asabar 18 ga wata ankai hari guda 1,481,847, a 20 ga wata kuma mahara sunkai hari 977,783
Abuja - Ministan sadarwa na ƙasa, Farfesa Isa Ali Pantami yayi wani iƙirari daya jijjiga zuƙatan yan Najeriya game da zaɓukan da suka gabata.
Pantami yace, an samu hari dake ƙoƙarin yin kutse a cikin ma'adanar tattara bayanai na hukumar INEC.
Harin yace, yazo ne daga ciki da wajen Najeriya, wanda adadin su yakai kimanin miliyan uku da dubu ɗari takwas da talatin da huɗu da ɗari biyu da arba'in da huɗu (3,834,244).
A cewar sa, an samu hari dake ƙoƙarin kutse kimanin 1,046,896 a ranar juma'a ta 17 ga watan Maris.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da aka samu wani ƙarin hari mai adadin yawan 1,481,847 a ranar 18 ta ranar asabar dake zaman ranar zaɓen gwamnonin da aka gudanar a watan na Maris din da muke ciki.
Duk da haka, maharan basu haƙura ba, domin ko a ranar 20 ga watan Maris na litinin, ai kaiwa ma'adanar tattara bayanai ta INEC sababbin harehare kimanin 977,783.
Hakan na zuwa ne ta bakin Dakta Femi Adeluyi, Babban Mataimakin Ministan Fasaha a ranar Laraba.
Babban mataimakin yace, Ministan sadarwa na ƙasa, ya kafa kwamiti dazai yaƙi da irin masu ƙoƙarin kutse a hajjojin hukumar INEC yayin gudanar da zaɓen na 2023.
A cewar sa:
"Abisa umarnin mai girma ministan sadarwa na ƙasa, kwamitin daya kafa tun kafin gabatowar zaɓe zai kula da duk wani abu da zai iya zuwa ya dawo akan tsaron yanar gizo gizo da kuma manhajojin hukumar INEC daga juma'a 17 ga Maris, 2023 zuwa litinin 20 ga wata 2023."
Ya ƙara da cewa:
"A wannan ɗan lokacin, mun tattara rahoton ƙoƙarin kutse da akai INEC na samfurin "DDoS" da "IPS", SSH da sauransu wanda adadin su yakai yawan 3,834,244, daga ciki da wajen ƙasar nan".
Jaridar The Sun ta ruwaito yadda Ministan sadarwan na ƙasa, ya tabbatar da cewa, aikin ɓata garin, yayi ƙaranci idan akayi la'akari da yawan adadin harin da aka samu yayin gudanar zaɓukan shugaban ƙasa dana ƴan majalisar dokoki da dattijai ta ƙasa.
Inda ya ƙarkare da cewa:
"Wannan abu ne mai ban mamaki, da yake zuwa a ƙasar da take da demokradiyya mafi girma a Afirka. Zaɓukan shugaban ƙasa dana majalisar dokoki da dattijai yafi ɗaukar hankali, shine abinda yatunzara yan fashin yanar gizo gizo kokarin yin illa ga tsarin na IREV a wancan lokacin idan aka hada da zaben gwamna da aka yi dana yan majalisar dokokin su." Inji sa
An yi Yunkurin yi wa Najeriya Kutse Kusan Sau Miliyan 13 Lokacin Zaben 2023 -Pantami
A ranar 25 na fabrairu akayi zaben sabon shugaban kasa, zaben da akayi raayi ya hadu cewae cike yake da kusakurai maras adadi daga ciki-wajen kasar.
Ita ma, Gwamnatin APC mai mulki ta tabbas daga akwai yanayim kalubale data fuskanta mai cike barazana iri-iri. Da suka hada da, kokarin mahara na'ura mai kwakwalwa nayi wa shafukan yanar gizon INEC mai yawan 12,988,978 kutse.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya fitar da jawabi a shafinsa, ya na bayyana haka.
Asali: Legit.ng