“Ma'aikatan Najeriya Ku Fita Zanga-Zanga Daga Litinin Saboda Ƙarancin Kuɗi” inji Kungiyar Kwadago

“Ma'aikatan Najeriya Ku Fita Zanga-Zanga Daga Litinin Saboda Ƙarancin Kuɗi” inji Kungiyar Kwadago

  • Zaɓe yazo ya tafi har yanzu ba'a fita daga cikin yanayin ƙarancin kuɗaɗe dake yawo a hannun jama'a ba
  • Ƙungiyoyin fafutukar kare yancin ma'aikata sun harzuka da lamarin da yake tafiya, samfurin tafiyar wahainiya
  • Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa ta umarci duk wani mamban ta daya shirya zanga-zanga daga sati me zuwa a ofisoshin CBN na kowacce jiha

Abuja - A Najeriya dai ana cigaba da fuskantar ƙarancin kuɗi tsaba na kashewa.

Hakan na zuwa ne tun bayan da CBN ya bada sanarwar canja fasalin kuɗi da kuma rage amfani da tsabar kuɗi.

Lamarin da bai yiwa ƴan ƙasa daɗi ba, wacce tasa har kungiyoyin fafutuka suka soma tasowa domin ganin CBN yayi abinda ya dace akan lamarin.

NLC2023
Yanzu-Yanzu: Ma'aikatan Najeriya Ku Fita Zanga-Zanga Daga Litinin Saboda Ƙarancin Kuɗi inji Kungiyar Kwadago
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

"Dama Haka Maza Suke?" Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ta Kwashe Kudinta Kaf Ta Tura Kasar Waje Ya Rabu Da Ita, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Wannan shine dalili da yasa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa tayi kira ga duk wani ma'aikaci ya ɗaura ɗamara ya dira a Ofishin CBN na kowacce jiha dake Najeriya domin gudanar da zanga-zanga.

Hukumar tace, lamarin zai gudana ne farawa daga sati mai kamawa idan har bata canza zani ba akan ƙarancin kuɗin kashewa da yayi katutu a cikin ƙasa.

Jaridar Punch ta rawaito yadda shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta ƙasa, Joe Ajaero ya sanar da hakan a wani ƙwarya-ƙwaryar tattauna da manema labarai da akayi a ofishin ƙungiyar dake Abuja.

Shugaban na NLC, yace umarnin ƙungiyar bai sauka akan kowani ma'aikaci ba, kuma ya zama dole saboda tun tuni suka bawa babban bankin sati ɗaya daya warware matsalar amma lamarin ya ta'azzara.

Biyo bayan ƙarewar lokacin, yace babu wani zaɓi face su ɗunguma shida ƴaƴan ƙungiyar na kowacce jiha zuwa ofishin CBN na kowacce jiha domin sauya akalar mahukuntan bankunan akan lamarin domin walwalar ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Mutuwa Ce Makomar Duk Mai Son Tayar Da Rikici a Ranar Zabe", 'Yan Sanda

Gwamna Ya Taya Tinubu Murna Bayan Kwana 21, Ya Nemi Bukata 1 a Gwamnatinsa

Gwamnan jihar Anambra ya fitar da wani jawabi, yana taya Asiwaju Bola Tinubu murnar nasara.

Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya ce tun da an lashe zaɓe, sai a maida hankali kan mulki, ayiwa yan ƙasa aikin da zasu kwashi romon demokradiyya.

Gwamna Soludo ya bada shawarar a fito da Nnamdi Kanu domin Ibo su iya samun zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar