Shahararren Fasto Ya Musanta Cewa Yace Mutuwarsa Ta Kusa
- Shahararren faston nan Cyril Chukwuemeka Odumeje ya fito ya ƙarya ta rahotannin ƙaryar da ake yaɗawa a kan sa
- Faston ya musanta cewa ya gayawa mabiyan sa cewa aikin da aka turo ya gabatar a duniyar nan ya kammala, don haka mutuwar sa na dab da zuwa
- Rahotanni dai sun bazu kan cewa shahararren faston yayi albishir da zuwan ranar mutuwar sa wacce a cewar su ta kusa zuwa
Jihar Anambra- Wani shahararren fasto a birnin Onitsa na jihar Anambra, Prophet Chukwuemeka Cyril Odumeje, ya musanta jita-jitar dake yawo cewa yace lokacin mutuwar sa ya kusa cika.
Lokacin da aka tuntuɓe shi a lambar wayar sa, ɗaya daga cikin hadiman sa wacce ta ɗauki wayar wacce ta bayyana sunan ta a matsayin Amaka Okoye, tace faston bai yi waɗannan kalaman ba. Rahoton Leadership
Ta bayyana labarin a matsayin ba komai bane face ƙanzon kurege.
A kalamanta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba gaskiya bane (cewa Prophet a lokacin al'amuran coci na Lahadi da ta wuce yace nan bada jimawa ba zai mutu)."
“Ƙasan cewa wasu mutanen idan suna son ɓata sunan wani za su ƙirƙiri wani rubutu su liƙa masa su sanya a Youtube su ce daga bakin sa abin ya fito."
Ta kuma bayyana cewa faston bai taɓa cewa ɗan sa, David, ya cigaba da riƙe ragamar gidan sa ba domin kwanakin barin sa duniya sun kusa cika.
A halin da ake ciki dai, wasu kafafen yanar gizo sun rahoto cewa faston a lokacin al'amuran coci na ranar Lahadi da ta gabata ya gayawa mabiyan sa cewa kwanan nan zai kammala aikin da aka turo shi yi a duniya.
A cewar rahotannin faston ya kuma umurci ɗan sa, David, da ya kula da iyalan sa da sauran abubuwan da yake gudanarwa a duniyar nan. Rahoton Vanguard
Sun Ki Allah Ya Nufa: Yadda Na Kusa Da Ni Suka Ci Amanata a Lokacin Zabe, Gwamnan APC Yayi Bayani Mai Sosa Rai
Shahararren Mawakin Najeriya, Alhaji Alao, Ya Mutu Yana Da Shekaru 121
A wani labarin na daban kuma, Najeriya tayi rashin wani shahararren mawaƙi da ya kwana biyu a duniya.
Mawaƙin mai suna Alhaji Alao ya rasu yana da shekara ɗari da ashirin da daya a duniya.
Asali: Legit.ng